Thursday, 26 December 2019

Yadda zaka/ki tsani wanda ka/ki ke so.

        A wani loqacin mutum yakan shiga wani yanayi tsakaninsa da masoyinsa/ta, wanda yake/take jin dama bata/baka san su tin da farko ba. Abin da yafi kyautuwa a gareka/ki shine kada ka/ki tsane shi/ta saboda soyayya da qiyayya dukansu yan’uwan juna ne, ko wanne kayi akwai damuwa. Abu mafi dacewa shine ka/ki cire su daga rayuwarki/ka, ma’ana, ka/ki yanke duk wata harqalla da kuke yi tsakaninku. Abin tambaya anan shine ta yaya zaka/ki yi hakan? Anan zamu maka bayanin hanyoyin da idan kabi su to babu makawa sai ka manta da lamarinsu gaba daya, sai dai loqaci bayan loqaci.

1. Ka/ki goge lambobinsu daga wayarki/ka, mafiya yawancin loquta zamu ga cewa mun haddace lambobin masoyanmu, to amma hikimar yin hakan shine, idan lambar na wayarka/ki zaka/ki iya canza ra’ayi ko wanne loqaci, amma idan ba lambar zaka/ki iya tinanin kafin ki/ka aikata hakan.

2. Ka/ki goge duk wani tattaunawa da kukayi ta kafafan social media (whatsapp, twitter, instagram da sauransu) ko kuma saqonnin karta kwana da aka saba turawa.

3. Ka dakatar da kiransu ta waya (blocking), hakan zai saka ko sun kira ka/ki bazata shiga ba, wanda hakan zai taimaka wajan manta su a rayuwarka/ki. Idan zai yiwu ma ka blocking dinsu a social media din.

4. Ka/ki yi tinani kafin ka/ki goge hotunanku domin wannan tarihi ne, wataqila wataran zaka/ki kalla ka/ki tina baya. Ki/ka yi dariya ko murmushi. Maimakon haka ka/ki samu wani waje ka/ki boye su domin gaba.

5. Ka/ki tattauna labarin naki/ka da wani abokin naki/ka hakan zai saka ka dan ji sauqin abinda ya faru.

No comments:

Post a Comment