Monday, 20 May 2019

YADDA ZAKA KWANA BAKAYI BACCI BA

    

Mafi yawancin dalibai ko ma’aikatan office suna so watarana kada suyi bacci da daddare saboda karatu, ko wani aikin office da suke so sun kammala ko kuma wani aikin da ya zama wajibi ayi shi a ranar, to kunga babu maganar bacci a wannan lamarin. Anan zamuyi bayani akan wanne hanyoyi mutum zaibi matsawar baya so yayi bacci.

1. Mutum ya cire tinanin duk wani abu daga zuciyar sa, tinanin ya hada da tilin aikin dake gabansa, ko wasu abubuwa daka iya dauke masa hankali, abinda zai dinga tinawa kawai shine, bafa zaiyi bacci ba sai kammala wannan aikin da ya zama wajibi a kansa

2. Shan abin da turawa suke cewa “coffee” yana matuqar taimakawa a kan wasu, shi wannan sinadir wanda duk aikin su daya da nescafi suna hana bacci matuqa gaya. Saboda haka shawara ga son kar yayi bacci, ya gwada yaga abin al’ajabi.

3. Idan baccin kaji yaqi sakinka, to sai ka dauko wayarka, ka kira wasu ku danyi hira na yan mintina, hakan yana saka wa baccin ya tafi domin ka ci gaba da aikin gabanka.

4. Ka dauki hutu yan mintina, ka fita waje, ka kalli taurari, domin su debe maka kewa, ka dan manta da abinda kake yi na wasu yan mintoci, hakan zai taimaka domin kwana bakai bacci ba. 

5. Watsa ruwa a fuska akai akai ko kuma tsoma qafa cikin ruwa duka hanyoyine na qin yin bacci da daddare. 

1 comment:

  1. Gaskiya muna godiya sosai ALLAH Ya taimaka ya kuma bada sa'a.
    don ALLAH Ina neman wata alfarma guda daya ka taimaka ka turomani fl studio mobile ta wannan lambar whatsapp din 09060335012 saboda wallahi nayi kokarin inyi dowmload nashi amman ko nayi download nashi nayi installing nashi zuwa wayata sai ya nuna mani download failed. Don Allah kataimakeni.

    ReplyDelete