Friday, 19 April 2019

Yadda ake daukar hoton kayan da ake siyarwa kuma suyi kyau sosai


Hotuna masu kyau hanya ce mai inganci sosai da za’a nuna kayan da ake siyarwa. Za’a fara ne da goge kayan domin suyi kyau sannan sai ayi amfani da gunkin mutum domin a dauki hoton ko kuma a kwantar dasu a kasa. A biyo mu domin sanin komai akan yadda ake daukar hoton kayan.
A takaice

Zamu tattauna akan wadannan abubuwan:
- A goge kayan da dutsen guga.
- A cire duk wani tabo ko datti daga jikin kayan.
- A duba kayan domin wasu matsalolin.
- Amfani da wayar hannu wajen daukar hoton.
- Amfani da Camera mai DSLR idan kana da daya.
- A dauki hoton kayan a farin haske ko kuma a saka kalar toka a bayan hoton.
- A dauki hoton kusa a taga domin haske daga rana.
- A karbi hayar Lightening Kit ko kuma a siya idan akwai kudi.
- A sami mannequin.
- A hayi tauraro idan akwai kudi.
- A matse rigar ta hanyar yin zanzaro ko kuma makale ta da allura ko pin.
- A kwantar da kayan domin nuna su ta hanya mai sauki.
- Daukar hoton gaba, gefe da kuma bayan kayan.
- Ka matso kusa domin nuna bayanai.
- A chanza tsayuwa yayin daukar hotunan.
- A duba hotunan domin zabar wanda ya dace.Mataki na daya: a fito da kyau na kayan.


1. A goge kayan da dutsen guga. Hakan zai sa duk wani yamutsewa da kayan sukayi ya tafi. Hakan zai sa kayan suyi kayu a idon masu siya.

2. A cire duk wani tabo ko datti daga jikin kayan. Idan akwai wani datti daya makale a jiki sai ayi kokarin cireshi, idan kuma an kasa sai a kaiwa masu wanki domin su cire wannan dattin, ba sai sun wanke kayan gaba daya ba.


3. A duba kayan domin wasu matsalolin. A duba kayan domin matsala kamar ta cirewar zare, zip, maballi da sauransu. Duk matsalar da aka gano sai ayi kokarin gyara ta.
- duk matsalar kuma da aka kasa gyarawa sai a rubuta domin a sanar da wanda zai sayi kayan.Mataki na biyu: shirya kayan aiki


4. Amfani da wayar hannu wajen daukar hoton. Wannan hanyar tana da sauki kuma ba’a kashe kudi wajen amfani da ita. A saka kayan a inda haske yake shigowa kamar wajen taga sai ayi amfani da waya wajen daukar hotuna kala-kala na kayan.


5. Amfani da Camera mai DSLR idan kana da daya. Yin amfani da DSLR yana sawa hoton yafi kyau kuma komai na jikin kayan ya fito sosai.


6. A dauki hoton kayan a farin haske ko kuma a saka kalar toka a bayan hoton. Domin komai na goton ya fito sosai za’a iaya haska shi da farin haske ko kuma saka takarda mai kalar toka a bayan kayan kafin a dauka.


7. A dauki hoton kusa a taga domin haske daga rana. Irin wannan hasken yana fito da kala sosai kuma ba biya zakayi ba domin a baka hasken. A sakale kayan ko gunkin a bayan tagar. Yafi kyau a dauki hoton da safe ko kuma da yamma.


8. A karbi hayar Lightening Kit ko kuma a siya idan akwai kudi. Akwai Lightening Kit wanda basu da tsada sosai, abu mafi muhimmanci a cikin kit din shine Softbox wanda yake gyara haske sosai ya cire inuwa da abubuwa da yawa. Idan sana’ar mutum ce siyar da kaya to yana da kyau ya malli kit din gaba daya.Mataki na uku: fito da kayan


9. A sami mannequin. Wannan shine kamar hoton gunkin da muke magan akansa. Yana da saukin daukar hoto kuma bashi da tsada a kasuwa. Akwai su kala-kala a kasuwa.


10. A hayi tauraro idan akwai kudi. Ganin kayan a jikin wani tauraro dayayi suna zai sa mutane suyi saurin siyan kayan, kuma zai bawa masu siyan fahimtar yadda kayan zaiyi musu idan suka saka a jiki.
- zaka iya sa abokinka ya saka kayan domin daukar hoton.


11. A matse rigar ta hanyar yin zanzaro ko kuma makale ta da allura ko pin. Idan an sakawa gunkin rigar sai ayi amfani da pin ko wani abu wajen matse rigar har ta zauna sosai a jiki. Musamman idan gunkin babu baya sai gaba kawai.


12. A kwantar da kayan domin nuna su ta hanya mai sauki. Zaka iya kwantar da kayan a kasa sannan ka dauki hoton a haka. Zaka iya saka wasu kayan ko tsummokara ko kwali a cikin kayan domin suyi tudu kadan.
- wannan hanyar tana aiki sosai akan kaya kamar rugunan sanyi, takalma, jakunkuna, skirt, tawul da kuma kayan yara.
- idan bazaka iya siyan gunki ba ko kuma ka hayo tauraro, to wannan hanyar tana da amfani sosai.Mataki na hudu: daukar hoton


13. Daukar hoton gaba, gefe da kuma bayan kayan. Idan kana amfani da gunki ne, sai ka dinga juya shi sannan ka dauki hoton ko wanne bangare na kayan, haka zalika idan ka hayi wani tauraro ne shima sai ya dinga juyawa kana daukar hoton.

14. Ka matso kusa domin nuna bayanai. Mutane suna son ganin komai na jikin kaya kafin su siya musamman idan a yanar gizo ne. Zaka iya matsowa gaba wajen daukar hoton ta hanyar daukar wajen maballai, kwalar rigar, wani zane dake jiki da sauransu.


15. A chanza tsayuwa yayin daukar hotunan. Idan wani ne ya saka kayan, yana da kyau ya dinga chanza tsayuwa kala-kala ana daukar hoton. Misali, ya saka hannu a aljihu, ko ya dora shi a kugu, ko a bayan wuyansa da sauransu.


16. A duba hotunan domin zabar wanda ya dace. Da zarar an gama daukar hotunan, sai a tsaya a tantance wadanda ya kamata a turawa masu siya sannan a goge sauran

No comments:

Post a Comment