Friday, 29 March 2019

Yadda zaku kula da tukunyar ku
Tukunya da muke dasu a cikin kitchen sunfi ko wanne abu aiki a cikin kitchen din. Sune muke amfani dasu wajen girka abinci. Idan basa kan risho to akwai abinci da aka ajiye a ciki bayan nan kuma zasu sha wahalar wanki. Yau zamu tattauna akan yadda zaka kula dasu kuma su dade suna yi maka amfani.

1. Idan ka siyo tukunya daga kasuwa, a wanke ta da ruwan zafi kafin a fara amfani da ita, sannan a bari tabushe daga nan kuma sai a shafa man kuli kadan a ciki. Hakan zai rage makalewar abinci sosai a cikin tukunyar.

2. Kar a dora tukunyar a kan wuta idan babu komai a cikinta. A tabbatar da cewa akwai ruwa ko mai a ciki kafin a dora a kan wuta.

3. A dinga dora kowacce tukunya akan wutar da ta dace. Misali, idan ana amfani da gas cooker a dinga dora karamar tukunya akan wuta karama. Idan ba haka ba wuta zata dinga yiwa tukunyar waya wanda zai iya jawowa hannun tukunyar ya balle da wuri.

4. Idan abinci ya kama a cikin tkunyar, a zuba ruwa da yawa a cikin tukunyar, sai a zuba garin sabulu a ciki, sai a dora ya tafasa. Hakan zai baka damar wanke tukunyar a saukake. Kar a dinga amfani da soson karfe wajen kankare abincin, domin hakan zai bada damar abinci ya kama nan gaba.

5. A dinga wanke tukunya da soso mai laushi. Amma kuma za’a iya amfani da soson karfe wajen wanke wajen tukunyar.

6. Kar a dinga saka tukunya a cikin oven idan hannunta na katako ne ko na roba ne.

1 comment:

  1. You telling good information about Gas Cookers check another best modern gas cookers Dubai from
    Gas Cooking Ranges I have had a good experience with them.

    ReplyDelete