Friday, 8 March 2019

Yadda Zaka Tambayi Kudi Daga Wajen Yan Uwanka (Kuma Su Baka)Yan uwanka sune mutane na farko da zasu taimaka maka idan ka shiga matsalar kudi. Yawancin zaka ji wani iri idan kana so ka tambaye su, amma domin saukaka abubuwa ka dinga fada musu ainahin abin da zakayi da kudin. Idan rance kake bukata, ka zauna da su, sannan ku tattauna nawa kake bukata kuma da lokacin da kake sa ran biya. Ku rubuta yarjejeniya domin kowa hankalinsa yafi kwanciya akan kudin.
A takaice:

Zamu tattauna akan wadannan abubuwan.
- Ka kidididdige komai da kake bukata.
- Ka tambayi rance a wajen mutanen da ka yarda dasu.
- Kar ka tambayi mutane da suke cikin matsala.
- Ka tattauna dalilin bashin.
- Ka tambayi dai dai kudin da kake bukata.
- Kayi bayani akan yadda zaka biya kudin.
- Ka tsara yadda zaka biya idan kudin yana da yawa.
- Ka kawo hukunci idan baka biya kudin ba yadda kukayi yarjejeniya.
- Kuyi rubutu.
- A dinga magana loakaci bayan lokaci.Kashi na daya: shirya tambayar kudin

1. Ka kidididdige komai da kake bukata. Duk lokacin da zaka tambayi wani kudi, ka dinga sanin nawa kake bukata. Yana da kyau kayi lissafi akan nawa kake samu a wata da kuma nawa kake kashw=ewa a cikin watan. Ka dinga rage kashe kudi. Misali, idan kaga cewa kana kashe kudi wajen cin abinci a waje, sai ka daina ka dinga girkawa a gida.

2. Ka tambayi rance a wajen mutanen da ka yarda dasu. Yawancin mutane wajen mama ko baba suke zuwa idan suna bukatar kudi. Kar ka dinga tambayar kudi a wajen wani kawunka da baku da wata alaka sosai domin kuwa babu lallai ma ya baka. Zaka iya rubuta wasika, ko ka tambaya a waya, amma kuma kaje ayi magana duska da fuska yafi tasiri.

3. Kar ka tambayi mutane da suke cikin matsala. Ka dauki lokaci wajen nazari akan wanda kake so ka tabaya kudi, shin shima yana cikin bukata ne? Kar ka dinga matsawa wanda tun asali yana cikin matsi.
- babban abokinka shine wanda zaka tambaya kai tsaye, amma kuma bai kamata ka tambayeshi ba idan shima yana kokarin biyan bukatunsa na yau da kullum.Kashi na biyu: tsara bashin

4. Ka tattauna dalilin bashin. Ka fadawa mutumin cewa kana so kuyi magana mai muhimmanci dasu. Ku zauna a wajen da babu wanda zai dameku sannan kayi bayani dalla-dalla akan dalilin da yasa kake bukatar kudin. Ka dinga fadin gaskiya a ko yaushe.
- misali, zaka iya cewa “Ina da kudin makaranta da ban gama biya ba, sannan kuma ga kudin haya da an biya” idan wannan ce matsalar taka.

5. Ka tambayi dai dai kudin da kake bukata. Idan da hali ka tawo da lissafin da kayi ko kuma reciept na kudin daya kamata ka biya. Sannan kuma kar ka tambayi kasa da yadda kake bukata domin kara zuwa karbar wani bashin bazai bada ma’ana ba.

6. Kayi bayani akan yadda zaka biya kudin. Ya danganta da yawan kudin da kake bukata da kuma kudin da kake samu duk wata. Misali, idan dan kudin cin abinci ne zaka iya biya cikin sati daya amma kuma idan kasuwanci zakayi, kudin zai kai kamar shekara ko watanni kafin ka biya.

7. Ka tsara yadda zaka biya idan kudin yana da yawa. Kamar yadda na fada a baya, idan kamar kasuwanci zakayi to kuwa ba lallai ka iya biya a lokaci daya ba. Yin tsari zai taimaka maka sosai.

8. Ka kawo hukunci idan baka biya kudin ba yadda kukayi yarjejeniya. Wannan ya rage gareka da kuma su, idan zasu dinga tina maka ne duk bayan kwana goma? Ko kuma su hanaka bashi idan baka cika alkawari wannan ba. Dai dai sauran hukunci da zaku yanke.

9. Kuyi rubutu. Ko musulunci ya yarda cewa ayi rubutun yarjejeniya idan aka bada bashi. Hakan zai sa ko matsala ta faru daga baya a magance ta.

10. A dinga magana loakaci bayan lokaci. Idan ka sami matsala wajen biyan kudin, ka kira kayi bayani kar ka tsaya har sai an kira ka.


No comments:

Post a Comment