Friday, 15 March 2019

Yadda Ake Girka Kisrat


Abubuwan da ake bukata:

- Masara
- Fulawa
- Yis
- Man KuliYadda Ake Hadawa

Zaa surfa masara sannan a jikata. Idan tayi kamar kwana biyu sai a wanke a kuma rufeta sosai. Idan na gari kike so sai ki shanya masarar taki. Bayan ta bushe sai ki bayar domin a nikota. Sai ki sami rariya mai laushi ki tankade sannan kuma ki sami garin fulawa shima ki tankade amma fa fulawar kada ta kai yawan garin masarar.
Idan kin gama sai ki hade su waje guda daya. Idan kuma kullu ne markade zaayi idan kin wanke masarar sai ki bayar a kai miki markade. Ammafa kar ki bari ayi miki markaden akan tattasai ko akan wani abun, idan aka kawo sai ki tankade fulawar ki zuba akai sai ki kawo ruwan yis wanda kika jikashi tun da dadedwa
sai ki kwaba da shi.

Amma fa ana son kullin da dan kauri bawai ki barshi ya yi tsilulu ba idan ya kwabu yayi yadde ake so sai a rufe a barshi domin ya
hau, sai a sami abin yin sinasir (tanda) marmara kamu wato non stick frying pan, sai ki shafa masa man Gyada idan ya yi zafi sai ki rinka zuba kullun a ciki amma da fadi akeyi kamar dai yadda sinasir yake. Idan ya soyu sai a sauke.
Ana iya cin sa da miyar farfesu, kubewa ko kuma wata miyar daban kamar ta ganye ko ta taushe.


No comments:

Post a Comment