Saturday, 30 March 2019

Yadda zaku iya magana a cikin mutane

Magana a cikin mutane, musamman masu yawa ba qaramin abu bane, shin maganar a cikin aji ne, ko kuma wani muhimmin taro a gurinka da dole se kayi Magana misali tron auran amininka. Kai kanka zaka so ace kayi wannan maganar ba tare da fargabar komi ba, ko tinanin wani abu, kuma zaka so ace mutane sun nishadu da maganganun da zakayi a wurin. Anan zamu kawo hanyoyin da zaku bi matuqar kuna so ku iya Magana cikin taron dubban jama’a ba tare da kunji kunya ko tsoron wani ba.

1.  Kasan akan me zakayi maganar. Misali in taron aure ne, to dole kasan tarihin mijin da amaryar tasa sosai, domin yin Magana ba tare da wani ya gane cewar baka san suba, ko kuma taron bude wani aiki ne, ko wani taron wani abu mai muhummanci.

2.  Ka rubuto abubuwan da zakayi bayanin a kansu ko a qaramar takarda ne saboda halin mantuwa,hakan zai qara maka kwarin gwiwa domin kana da rukunonin abubuwan da zakayi bayanin a kansu.

3.  Ka/ki yi qoqari ka haddace abinda zakayi bayanin akansa, ko da  baka haddace ba duka ba, ya zamanto cewa abubuwan dab aka haddace ba kana kallon rukunin bayani zaka tina komi a kansa.

4.  Kasan suwa zaka yiwa bayanin, domin abinda zai bawa wasu dariya, wasu in ka fada haushi zai basu, misali; abinda zaka fadawa daliban firamari su nutsu su saurareka bashi zaka fadawa daliban jami’a ba, domin se suyi maka kallon solobuyo.

5.  Ka kula da harshen ka,wato yanayin kalmomin da kake fada a wurin, ka sani cewa irin maganganun da zakai a wurin taron siyasa ba iri daya bane da wanda zakayi a wurin taron farfesoshi, ko taron addini ba.

6.  Ya zamanto cewa baka cukulewa, ma’ana ka yawaita fara’a domin hakan zai saka masu sauraronka su dinga jin dadin sauraron naka.

7.  Kada kayi shiga kamar wani almajiri, ko kuma mawaqee a wurin da kasan taron malamai ne,kada kayi shigar alarammomi a wurin taron ma’aikatan lafiya, ma’ana dai yanayin shigar da kayi yanayin mutuncinka a idanun masu sauraronka.

8.  Ka dinga kawo misalai da abubuwan ban dariya a inda ya dace, kayi Magana a nutsi bada sauri ba, ta inda kowa zaiji dadin sauraronka

9.  Ka yi qoqari wajan bada bayanin ka, ka saka yan labaruruka wadanda suka danganci abinda kake bayanin a kansu, domin mutane suna son labara, hakan zai saka hankalinsu gaba daya ya kawo kanka.

10.  Abu na karshe ka tabbatar qarshen maganar ka yayi kyau, domin mafi yawancin mutane sunfi tina abinda aka fada musu a farko da kuma qarshe, idan sunji dadin qarshen maganar to zaka ga har wadanda basa maida hankali sai sun nemi a yi musu qarin bayanin abubuwan da ka fada.

No comments:

Post a Comment