Monday, 25 February 2019

Yadda zaku daina tinanin abinda ba kwa so ku dinga yawan tinani a kansa


Mutane da yawa suna so su daina tinanin wani abun da yake saka su damuwa, kuma sun kasa cire tinanin daga zuqatansu saboda bazasu iya gaya wa wani abin ba.  Hakan ka saka wa mutun wata cuta wacce zata iya taba lafiyarsa ko tinanin sa baki daya, wanda hakan ba daidai bane. Anan zamu duba yadda za ka/ki iya cire wannan tinanin daga zuciyar ki/ka.

1. Ya zamanto cewa ka/kin samu wuri wanda ba jama'a da yawa a wujan, musamman wajan da yake dauke da abubuwan sh'awa, kamar wurin shaqatawa, bakin teku da sauransu.  ka/ki nutsu, samu kujera ko wurin zama mai kyau, ka/ki tankwashe qafa idan a qasa ka/kika zauna, jaa numfashi sosai ya zamanto cewa hankalin ki/ka ya tattaru a wuri daya, ka/ki maida hankali a yanayin wurin, irin ni'imar da Allah yayi wa wurin da abubuwa makamancin haka, yin hakan zai saka ka/ki shagaltu da irin wadannan abubuwa domin mantawa da abinda ke damunki/ka.

2. Ka/ki shagaltu da wasu abubuwan da ka/kika kware a kansu akansu, misali, idan ka/kin kware wajan iya karatun littafi, ko rubuce rubuce, ko kuma dai wani abun da in ka/ki na yi zai saka ki/ka manta da komi sai wannan abin da ka/kike yi a wannan loqacin.

3. Ki/ka dinga rubuta abinda ka/ki ke so ka/ki daina tinanin a kansa, saboda rubuta abu ko fadawa wani yana sawa ka/ki daina tinanin abin.

4. Ka/ki dinga yin wasannin da suke tafiya da hankalin mutun misali "puzzle" a turance, domin wasanni ne da suke buqatar tattara hankali da tinani domin yin su.

5. Ka/ki dinga yawan motsa jiki, domin motsa jiki ya kan sa ka/ki manta damuwa da wasu abubuwan da ka iya baka matsala cikin tinanin ka/ki.

6. Ka/ki yawaita abokayan ki/ka ziyara don ku tattauna akan wasu abubuwa, ku fita yawon zagaye gari, ku ji dadi, kuyi wasa da dariya ku more rayuwarku. Hakan zai saka ka daina tinanin komai in ba abinda ya faru a ranar ba.

No comments:

Post a Comment