Saturday, 23 February 2019

Yadda zaka saka maihaifinka farin ciki (a saukake)Kowanne da na gari yana san mu’amala ta farin ciki da babansa. Idan maihaifinka yana farin ciki da kai, zaka samu kulawa sosai daga wajensa sannan kuma kaima zaka kasance cikin farin ciki. Akwai lokutan da sa masa farin ciki yake da matukar wahala.


A takaice

Abubuwan da zamu tattauna sun hada da:
- Ku kashe lokaci tare.
- Ka guji jayayya.
- Ka nemi shawarasa.
- Ka nuna masa kauna.
- Ka dinga kwaikwayon hayensa masu kyau ko kalamai da ya saba fada.
- Ka dinga ayyukan gida.
- Ka fara sabon abu.
- Ka dinga tsaftace dakinka.
- Ka dinga amfani da yanar gizo da wayarka da tinani.
- Ka lura da ‘yan uwanka.
- Kayi karatu da kyau.
- Ka dinga girmama malamanka.
- Ka dinga shiga sauran wasanni da kungiyoyin makaranta.
- Kayi abokanai na gari.


 Mataki na daya: Zaman tare


1. Ku kashe lokaci tareYana da wahala ku dinga kashe lokaci da maihaifinka musamman idan kana zuwa makaranta shi kuma ya tafi wajen aiki. Jajircewa da samun lokaci ko yaya yake da zaku zauna ka fada masa ra’ayinka da abinda ke ranka yana da kara dankon soyayya tsakanin ku. A kalla ku dinga cin abinci tare a rana koda sau daya ne. Wannan yana iya zama lokaci mai kyau da zaku tattauna abubuwan da suka faru a ranar, abinda ke damunka ko kuma abinda ma ke ranka gaba daya. Idan shima maihaifin naka mai bada labarin abinda ya shafe shi ne, sai ka nuna masa cewa kana jin abinda yake fada maka. Misali, idan ya baka labarin abinda yake damunsa zaka iya tambayarsa akan wannan abun bayan dan lokaci.

- ka koyi abubuwa daga rayuwarsa. Ka dinga tambayarsa akan kuruciyarsa da kuma samartakarsa, abubuwan da yake so, burin dake ransa a lokacin, abubuwan da bazai taba mantawa dasu ba da dai sauransu. Wannan labaran zasu taimaka maka idan ka girma. Zama su iya taimaka maka wajen kara ganin kimarsa da muhimmancinsa.

- ka dinga sauraronsa da kunnenka sosai. Sauraro yana nuna ka damu sannan kuma yana kara soyayya.

2. Ka guji jayayya. Yana da matukar wuya kayi shiru akan abinda ya fada wanda baka yarda dashi ba ko kuma kana san kayi wani abu shi kuma ya hanaka. Ka nutsu sannan ka kama kanka idan yana yi maka magana da baka so. Ka dinga jira sai ka sauko sannan ka sameshi kuyi magana. A koda yaushe ka dinga kokarin fahimtar ra’ayinsa domin kuw akoda bai haifeka ba, ai ya girmeka. Abinda kake tinanin ya hanaka yi zaka gane cewa soyayya ce ta jawo hakan nan gaba.

- Idan kaga yana cikin fushi, ka dinga tinanon abubuwan da suka saka shi fushin kamar ko ya gaji ne, ko yana jin yunwa ne, a lokuta da dama ba kaine ka sakashi fushin ba.

3. Ka nemi shawarasa. Ka dinga neman shawararsa akan makaranta, abokanai, neman aiki ko kuma kashe kudi. Hakan zai nuna masa cewa kana bukatar ra’ayinsa. Koda ace bashi da ilimi ko kwarewa akan abinda kake tambayar shi, zai iya baka shwarar da zata taimaka akan yadda zakayi ko kuma ya fada maka wanda zaka samu.

4. Ka nuna masa kauna. Ka dinga nunawa maihaifinka cewa kana sanhi. Ka dinaga yi masa magana da lafazin nuna so, zaka iya rungumarsa. Yawancin yara maza sunfi jin kunyar nunawa maihaifinsu soyayya. Ka nemi abinda ya dace na nuna masa kauna. Idan ba sai ka dinga rungumeshi a cikin mutane ba idan kana jin kunyar yin hakan.

5. Ka dinga kwaikwayon hayensa masu kyau ko kalamai da ya saba fada. Ka samu kayi lissafin abubuwan da yakeyi masu kyau ko kuma wasu halaye ko maganganu da ya saba yi. Misali idan ya saba cewa ‘Gaskiya bata karewa, karya ce mai karewa’ ko kuma ‘Mutum ya dinga iya kokarinsa idan zaiyi abu’. Amma ba lallai bane ace ko da yaushe yake fadar irin wadannan kalaman, watakila sai kun zauna lokaci bayan lokaci. Ka dinga lura da yadda yake cika alkawari, yake saurin shiryawa ya fita wajen aiki, da kuma yadda yake saka kaya masu mutunci. Kaima ka dinga gwadawadannan halayen a rayuwarka.

- ba lallai bane ace ka yarda da duk abinda yake fada maka ko yake aikatawa ba. Ka dinga kwaikwayon halayensa da zasu taimakawa rayuwarka. Idan yana da hanyar yin wani abu wanda zuciyarka bata kwanta dashi ba, zaku iya zama domin ku tattauna watakila ya daina yin wannan abun.Mataki na biyu: Yin dawainiya a gida


6. Ka dinga ayyukan gida. Kayi tinanin aikin da mahaifinka yake yawan saka ka. Ka kara yin tinanin ayyukan da kai kasan kaine ya kamata ka dinga yinsu. Idan baka jin dadin yin ayyukan gida ko kuma suna baka wahala, sai ka nemi shawarar mahaifinka akan yadda zaka dinga yinsu a saukake. Zai iya baka shawara akan hanya mai sauki da zaka dinga yin aikin.

- Neman shawararsa yana nufin kana darjta ra’ayinsa. Da zarar maihaifinka ya baka shawara, kayi aiki da ita. Zaiga cewa ka raina shi idan ka nemi shawararsa sannan kuma kaje kayi gaban kanka.
- ka dinga kokarin kin bawa mahaifinka damar tambayarka dalilin daya sa bakayi ayyukanka na gida ba. Ka dinga yinsu koda yaushe, zaka iya hada jadawalin lokutan da zaka dinga yinsu. Ko kuma ka dinga saka alarm masu yawa a wayarka da zai dinga tina maka cewa lokacin aiki yayi.

7. Ka fara sabon abu. Ka dinga lura da ayyukan gida wanda babu wanda yayi kuma babu wanda aka ce yayi su. Ka dinga bawa maihaifinka mamaki ta hanyar yinsu. Ka kara tinanin aikin da ya dade ba’ayi ba kuma babu mai niyyar yinsa a gidan misali share yanar gidan.

- ka dinga lura da abubuwan da yake so a wasu lokutan, misali idan yana so a dinga wanke masa mota kafin ya tafi wajen aiki, sai ka dinga yi masa. Hakan zai num=na masa cewa kana da tinani.

8. Ka dinga tsaftace dakinka. Yawancin iyaye suna fada akan yadda yaransu basa tsaftace dakinsu. Ko da ace kai kadaine a cikin dakin, yana da kyau ka nunawa maihafinka cewa ka iya daukar dawainiyar abinda yake naka ne ta hanyar shareshi da tsaftace shi.

- ka dinga gyara gadonka kullum da safe idan ka farka, sanna kuma kar ka dinga hade kayanka masu kyau a cikin kayan wanki. Idan kuma zaka yin like-liken takardu a jin bango, kar ka saka hoton da kasan zakajin kunyar mahaifinka ko wani babba idan ya shigo dakin naka.

9. Ka dinga amfani da yanar gizo da wayarka da tinani. Idan mahaifinka ya kasance shine yake siyo maka data kuma yake saka maka katin kira. Ka sani cewa amfani da waya ko kuma shoga yanar gizo alfarma ce ake yi maka ba hakki bane da dole sai an baka. Ka nuna masa cewa kana ganin muhimmancin kudin da yake kashe maka kuma kasan darajar tarbiyar da yayi maka.
- ku tattauna ka’idoji da mahaifinka akan amfani waya, game da sauransu. Lokacin da ya kamata ka kashe su domin bacci, irin abubuwan da zaka dinga sakawa a yanar gizo da sauransu.

- ka guji amfani da wayarka idan kuna cin abinci domin hakan yana nuna raini.

10. Ka lura da ‘yan uwanka. Ka bawa maihaifinka kwanciyar hankali idan ya dawo gida. Ka dinga kokarin zaman lafiya da ‘yan uwanka. Kar ka dinga cin zalin kannenka sann kuma kar ka dinga fada da yayyenka. Ka dinga taimaka musu da aikin makaranta daaka basu. Ku dinga wasannin nishadi tare, sannan idan kana iya tuka mota ka dinga kaisu uwanguwa ba sai mahaifinka ya kaisu ba.Mataki na uku: Yin kokari a makaranta.


11. Kayi karatu da kyau. Ka dinga nunawa mahaifinka cewa kana san ci gaba a rayuwa ta hanyar kokari a makaranta. Ka dinga kokarin yin duka ayyukan gida da aka baka daga makaranta. Idan akwai abinda baka gane ba, ka tabbatar ka kara tambayar malaman makarantar.

- ka tsara jadawalin aikin gida da kuma sauran ayyukan ka.
- ka tsara jadawalin karatu. Misali, minti 45 na karatu sai kuma mintuna 10 na hutawa. Ka dinga kashe wayarka idan kana karatu.
- ka nemi daki wanda babu surutu domin kayi karatu.
- ka shirya littatfanka.

12. Ka dinga girmama malamanka. Idan kana yi musu magana ka dinga yi da ladabiu. Ka nuna musu tarbiyyar kirki da akayi maka a gida. Maihaifinka zaiyi farin ciki sosai idan yaji malamai suna yabonka.
- hakan baya nufin cewa sai ka yarda da duk abinda malaminka yake fada ko kuma yake aikatawa. Idan kaga yana yin mugunta ko yana saka ku abinda bai dace ba, zaka iya samun shugaban makaranta domin ka kai kara. Ka tabbatar cewa sujma mahaifanka ka fada musu domin su san abinda yake faruwa a rayuwarka.

13. Ka dinga shiga sauran wasanni da kungiyoyin makaranta. Makaranta ba wai kawai shiga aji bane a koyar da kai lissafi ko turanci. Yin sauran ayyukan makaranta yana kara sawa ka zama mutum sosai. Zasu taimnaka maka wajen shirya abubuwa, shugabanci, aiki tare, hadin kai, zama da mutane da sauransu. Wannan kadan daga cikin abubuwan da mutum yake bukata ne domin ci gaba a rayuwa, kuma duk iyaye suna so suga yaransu suna ci gaba.

14. Kayi abokanai na gari. Ka nunawa mahaifinka cewa kana gane dabi’a mai kayau daga mara kyau. Ka dinga abokantaka da mutane da suke da kokari a makaranta. Ka nemi wadanba suke da dabi’a mai kyau domin kuyi abokantaka. Ka nemi wadanda basa jan rigima domin kaima ka zama irinsu. Kar ka kuskura ka dinga yin abu wai dan kawai abokananka suna yi. Ka dinga tinani akan abubuwa kafin ka aikata. Idan kana samun matasalar abokanai sai kuyi magana da mahafinka domin ya taimaka maka.
No comments:

Post a Comment