Sunday, 17 February 2019

YADDA ZAKU DAINA JIN KUNYA A GABAN MASOYANKUKunya ba wani abun aibu bane da mutane zasu dinga guje mata, bal ma abu ne mai matuqar kyau ace mutum yana da ita, musamman ga mata, har mazan ma a wasu loqutan. Matsalar itace ta yaya zamu daina jin kunya yayin da muke tare da masoyan mu. Ko wanne mutum yana so wanda suke soyayya ya/ta zama ta/ya na sakin jiki da shi ko ita. 
To ga hanyoyin da zaku iya bi domin rage kunyar da kuke ji yayin da kuke zaune da masoyanku a ko yaushe. 

1. Ya zaman to munsan banbancin kunya da kuma kawaici.
Kar ka/ki taba bada haquri saboda ki/ka na jin kunyar masoyiyarka/masoyinki.  Ka/ki sanar da shi/ita cewa jin kunya fa ba laifi bane, sanin mai zaka/ki kunya akai shine matsalar. 

2. Ku yawaita zama a cikin 'yan uwa da abokan arziqi wadanda bakya/ka jin kunyar su domin saka ka cikin nishadi da jin dadi, hakan zai saka ka/kk rage jin kunya a loqacin da kuke zaune tare masoyanku. 

3. Ka/ki zama kuna yawan tattaunawa ta yanar gizo gizo (facebook, twitter, whatsapp, instagram)  da sauransu,  domin mafi yawanci zamu ga cewa idan muna zaune a wuri daya ne muke jin kunya idan muna magana, amma in a social media ne bama jin wannan kunyar, wato ba kamar muna ganin mutum bane. 

4. Idan zaka/ki iya ki/ka samu takarda ka/ki rubuta irin abubuwan da zaku tattauna kafin ko wacce haduwa, sai ka/ki dinga kwaikwayon yadda zaki/ka dinga maganar a gaban wani abokin/qawar  ki/ka   yin hakan zai rage kunya yayin da kuke tattaunawa. 

5. Ko yaushe idan masoyinki/masoyiyarka masu son surutu ne, to kada ku kuskura ka/ki dakatar dasu idan suna yi, ka/ki saurari abin da suke fada kuma ka/ki dinga yawan nuna cewa ki/ka na gane abin da suke magana akai koda kuwa ba hakan bane. 

6. Ka/ki dinga qoqari ka/ki na hada ido dashi yayin da ya/ta ke magana, yin hakan na rage jin kunya sosai har ta kai ga wataran za ka/ki iya kallon sa/ta na tsawon loqaci ba tare da jin wani abu ba.

No comments:

Post a Comment