Sunday, 17 February 2019

Yadda zaka kula da shanunka
Wasu suna son kiwon shanu sai dai basu san ta yanda zasu fara ba,  ko kuma ba su ya ake kiwon ba saboda basu taba yi ba. To anan zamu nuna yadda zaka kula da shanun ka matuqar baka son kasha wahala kuma kana so kayi kiwon ka cikin nishadi da jin dadin ka tare dana shanun. 1. Da farko dai san samu ka samu fili a qalla aaka biyu (2) domin ciyar da shanun da kiwon kiwon su. 

2. Idan filin ka bai kai aaka 2 ba ga ko wacce saniya guda 1 to ya zama wajibi ka samar da hanyar da zaka dinga bawa shanun nan abincin daga wata hanyar, a taqaice ka dinga suwo musu. 

3. Yana da kyau da raba filin naka gida 2 ko fiya, ya danganta da filin, sabida samar da ciyawa mai yawa domin shanun, musamman idan an samu tsaikon saukar ruwa da wuri, hakan zai sauwaqe maka wajan wahalar naiman musu abinci.

4. Yana da kyau ka kewaye filin da kake kiwon nasu saboda barna, kuma idan ka tashi yin kewayar,  to ka saka waya ba katanga ba, saboda ita ce zata baka daman yin canje canje,  a duk loqacin da kake so ka qara girman filin ko ka rage shi. 

5. Ya zama dole ka tanadarwa shanun ka wurin shan ruwa mai kyau, idan wurin yayi datti ka wanke shi. Kuma ruwan shima ya zamanto mai kyau. 

6. Ya zama wajibi abincin da zaka basu ya zama ya cika duk wani sharuda na abinci mai kyau, saboda hakan zai rage musu saurin kamuwa da cututtuka. 

7. Ya zama wajibi ka tanadar wa dabbobinka likita, kuma ka tabbatar duk wata matsala na faruwa shi wannan likitan dabbobin zai zo ya duba su.

8. Ka tanadar wa shanunka hanyar samun gishiri, domin suna buqatar abinci mai dauke da sinadarin da ake kiransa "calcium" saboda qara musu kwarin qashi da lfya sosai. 

 9. Yana da kyau da sabar wa da shanun ka wani kalar sauti da suna ji sun san kai kake kiransu domin basu abinci ko abin sha ko son ganinsu

10. Kada ka kuskura ka dinga bawa shanun ka wahala sosai, ta yanda zasu rinqa ramewa ko su tsane ka sanadiyyar basu wannan wahala da kake.

No comments:

Post a Comment