Tuesday, 26 February 2019

Yadda zaka amsa " A ina ka samu lamba ta" yayin da wata ta tambayeka.

Maza da dama suna samun matsala yayin da mace ta tambayesu "a ina ka samu lamba ta? ".  Saboda qila baka son fada, qila kuma wanda ya baka lambar ya gaya maka cewa kada kace shi ya baka, ko kuma bai fada maka haka ba, kawai kai kake ganin bai kamata ka fada mata ba. To ican ka tsinci kanka irin wannan yanayin, yana da kyau kayi duba sosai da nutsu kafin ka bada amsar, dalilina kuwa shine. Wata ba damuwa tayi da a ina ka samu ba, ko waye ya baka, kawai tana so ta gwada yanayin amanar ka da gaskiyarka, wata kuma abinda take so taji kenan, kuma na tabbatar cewa baza kaso ace tattaunawar da kuke ta tsaya a nan ba. 

Abubuwan  da zaka duba kafin ka bada amsar sune. 


1. Ka zama mai gaskiya, ka nemo hanyar da zaka saka tattaunawar taji gaba, ba tare daka bata waccan amsar ba. Misali, tana maka tambayar, sai kace mata, " ai kamata yayi ki tambayeni wahalar da nasha kafin in samu numbar" ko kuma "kamata yayi ki tambayeni, me yasa na samo lambar ki ba a ina na samu ba".  Tambayoyin dai da zasu saka ba kai mata qarya ba kuma baka bata amsar ba. 


2. Ka fara yabonta da irin kyan da take dashi, ko wani abin da kasan tana da shi. Domin ba macen da bata son yabo a duniyar nan. Ka nuna mata cewa ai lambar ta bazatayi wahalar samu ba tinda tana kan kafafan sada zumunta na facebook da sauransu. 


3. Kada ka nuna mata cewa kana da ra'ayin bin mata irinta yayin da kake tsakiyar bayanin, domin hakan zai saka tattaunawar ku ta qare a wannan loqacin.

1 comment: