Saturday, 16 February 2019

Yadda albasa take da amfani a wurin bacciMutane nasan zasuyi mamaki akan mai zai saka mutum ya kwana da albasa a cikin qafarsa. To in buku sani ba bari na fahimtar daku. Shin ko  kun taba ganin masu saka albasa a cikin safa (socks)  yayin kwanciya, to hakan ba shirme bane, bal ma qarin lafiya ne. 

Nasan wasu zasu tambaya me yasa mutum zai haka? Dalili shine jijiyoyin da suke jikin albasa suna bada alfanu sosai wajan shigar da sinadaran da suke cikin albasar zuwa jikin mutum kai tsaye, domin amfani. 

Masana sun yi binkice mai zurfi sun gano cewa kwanciya da albasa a cikin tafin qafa yana qara abubuwa kamar haka:

1. Kwana da albasa a cikin tafin qafa yana taimakawa wajan yaqi da cututtuka masu yawa. 

2. Yana taimakawa wajan wanke jinin jikin dan adam. Wanda hakan kan qara lfya ga shi kansa dan adam din. 

3. Yin hakan na taimakawa wajan gudanar da gudun jini yanda ya kamata. 

4. Yana taimakawa wajan rage warin tafin qafa sosai. 

5. Yana taimakawa wajan fitar da ruwan jikin dan adam wanda ba'a buqatar sa. 

Ku gwada hakan na kwana 5 ku sha mamaki gaske.

2 comments:

  1. nagode kwaraida gaske kuma nakaru sosai ta yadda zan ingnta lafiyata

    ReplyDelete
  2. Tabbas zan gwada tare da sanar da mutane Domin lafiyarsu

    ReplyDelete