Tuesday, 22 January 2019

Yadda zaka kashe wayarka yayin data maqale

A zamanin yanzu da aka yo wayoyi wadanda batirinsu a ciki yake, wato bazaka iya ganin batirin ba ballantana ka cire shi, mutane masu irin wadannan wayoyin suna shiga damuwa yayin da wayoyinsu suka qi kasuwa a loqacin da suke amfani da ita kuma ta maqale wato abinda muke cewa hooking. Wasu loquta idan mutum ya saka qararrawar tinasarwa (alarm), musamman in ya kashe wayar, akan samu akasi ta maqale, wani loqacin kuma bama sai ka kashe wayar ba, wasu loqutan kana kan ganiyar amfani dasu, ta yiwu lodi ne yayi mata yawa ko kuma an bude application da yawa kawai sai kaga taqi gaba taqi baya.

To abinda zaka/ki yi ba wani abu bane mai wahala, abu ne cikin sakanni qalilan zaka/ki gyara wayarka/ki ta koma daidai cikin kwanciyar hankali da ruwan sanyi. Kai idan kaso ma kana kwance ba tare da motsa daga inda kake ba, kuma ba tare da ka je wajan mai gyara ya cima kudi a banza ba.

Hanyar da zaka/ki bi itace:
Zaka/ki riqe wayar ka danne wurin qaro qarar waya (volume) na sama tare da makashi/makunnin waya (switch) a loqaci daya, zaka riqe su har tsawon sakan goma. Kana yin hakan zaka ga ta dauke, sai ka saki domin ka jira kawowar ta.

                                   

1 comment: