Saturday, 5 January 2019

Yadda Ake Sawa Yaro Ya Daina Fitsarin Kwance


1. A jira har yaro ya isa. wataƙila yaronki ya koyi zama da rana ba tare da ya bata wandonsa ba, hakan baya nufin cewa zai iya bacci da dare ba tare da yayi fitsarin kwance ba. Yana da kyau a dinga amfani da pampers ko napkin a lokutan da yaro zaiyi bacci domin gujewa fitsarin kwance. Ki gane cewa ɗabi’un yara ya banbanta.

2. Amfani da katifa mai leda. Idan bazaki iya amfani da napkin ko pampers ba, to yana da kyau ki sayo katifa mai leda ko ki sakawa taki katifar leda domin gujewar lalacewa.

3. Ajiye zanin gado da sabon wando a kusa. Idan yaro yayi fitsarin kwance, yana da kyau a cire masa kayan daya ɓata, tare da chanza zanin gadon da yake kwance akai.4. Kar ayi hantara ko duka. yana da kyau ki gane cewa fitsarin kwance kusan dole ne a wajen yara, duka ko hantara bazai sa yaro ya daina ba. Abu mafi kyau shine a ƙarfafi yaro, a faɗa masa cewa zai daina zuwa wani lokaci

5. A rage shan abu mai ruwa kafin a kwanta. A tabbatar cewa yaro yana shan ishasshen ruwa da rana. Amma da dare yayi sai a rage bashi ruwa. A guji bawa yara soda, coke ko nescafe da dare, saboda suna sawa ayi fitsari.

6. A kai yaro bandaki kafin ya kwanta. A ƙarfafawa yaro gwiwar zuwa banɗaki yayi fitsari kafin ya kwanta. Hakan zai rage masa ruwan dak cikin mafutsararsa.

7. Kwanciya a ƙayyadajjen lokaci. fitsarin kwance yana faruwa ne saboda jayayya tsakanin kwakwalwa da kuma mafutsara. Saboda haka kwanciya da tashi a ƙayyadajjen lokaci zai koyawa mutum riƙe fitsari a wannan lokacin.

8. A kula da abinda yaro yake ci. akwai kalar abincin da sukan jawo matsala ga yara, koda kuwa matsalar bata bayyana a matsayin kuraje ba ko wasu alamomin. Misalin waɗannan kayan abincin sun hada da abinci mai acid a ciki da kuma abinci da yake da madara, waɗannan sukan hana yaro farkawa idan mafutsararsa ta cika.
9. A bawa yaro calcium da magnesium. binciken masana ya nuna cewa idan jikin yaro babu calcium ko magnesium hakan zai iya jawo masa fitsarin kwance. Saboda haka a dinga bawa yara abinci kamar ayaba, kifi, wake, riɗi, da sauransu.

10. A tashe shi daga bacci. babu laifi idan aka tashi yaro daga bacci domin ya shiga banɗaki yayi fitsari da dare ko kuma asaita masa alarm domin ya tashi da kansa.

11. A guji sanyi. jin sanyi ga yaro idan yana bacci zai jawo masa yin fitsari a kwance. Saboda haka a tabbatar yaro yana cikin ɗumi idan yana bacci.

12. A dinga rubutawa. idan yaro yaci gaba da rigimar yin fitsarin kwance, zaki iya rubuta lokotan da kika san yana yin fitsarin da kuma yanayin da yake yi. Hakan zai taimaka wajen fahimtar ɗabi’ar yaronki idan yana bacci domin ki tashe shi ya shiga banɗaki.

13. Magana mai daɗi. ki sani cewa yara suna fitsarin kwance ne bada saninsu ba. Saboda haka magana mai daɗi zata taimaka musu wajen dainawa, saɓanin zagi ko cin mutunci.

14. Wanka da gishiri. idan aka zuba gram  kamar dari baiyar na gishiri a cikin ruwan wankan yaro na dare zai rage masa kamuwa da wasu kwayoyin cuta, ƙarfafawa sojojin jikidake yaƙar cuta a cikin jiki, sannan kuma ya cire datti dake cikin jini. Hakan zai yi aiki akan fitsarin kwance idan matsalar daga mafitsara ce.

15. A bashi shayin ganyen parsley (faski). za’a iya bawa yaro ruwan ɗumi da aka zuba busasshen ganyen parsley (faski) aciki amma a bari faskin ya jiƙu kamar zuwa mintuna biyar sai a tace. Sai a saka lemon tsami da zuma kadan. A tabbatar da safe aka bawa yaron shayin da dare ba.

16. A bashi shayin gashin jikin masara. A abri gashin jikin masarar ya bushe na wasu kwanaki sannan ayi shayi dashi ta hanyar rufe shi a cikin tafasasshen ruwa tare da barinsa ya jiƙu zuwa mintuna 10. Shima wannan shayin a tabbatar da safe aka bawa yaron shayin da dare ba.
17. A lura da lokacin ganin likita. fitsarin kwance ba matsala bane ga yara da har za’a je wajen likita. Amma
- za’a iya ganin likitan yara idan yaro ya wuce shekaru 7 kuma yana fitsarin kwance. Likitan yara zai bada shawarwari sannan kuma ya tabbatar cewa yaron bashi da matsalar mafitsara.
- za’a iya ganin likitan yara idan yaro ya wuce shakaru 5 amma kuma yana fitsari har da rana ba dare kawai ba.

No comments:

Post a Comment