Saturday, 5 January 2019

Yadda Mutum Zaiyi Idan Yaki Yin Azumin Ramadana Da GanGan

Tambaya: Idan mutum mai lafiya yaki daukar azumin Ramadana da gan-gan babu wani uzuri, menene hukuncinsa?

Amsa: A hakikanin gaskiya baza’ace mutum ya fita daga musulunci ba, amma kuma ya aikata babban zunubi (kaba’ira) kuma abinda za’a fadawa masu irin wannan halin shine abinda manzan Allah ya bada labari da kansa cewa yayi mafarkin wasu mala’iku sunzo su biyu sun tafi dashi suna cikin tafiya sai suka zo wajen wani katon dutse, yana ganin ya zaayi ya hau wannan dutsen sai sukace masa zasu taimaka masa ya hau. Bayan sun haye dusten kuma sai aka nuna masa wasu mutanen a chan wutar jahannama an rataye kafafunsu a sama, kansu na kasa, wuta tana ci daga karkashinsu, wuta na fitowa daga bakinsu, anayi musu azaba. Sai manzan Allah ya tambaya wadannan wane mutane ne? Sai akace masa wadannan sune mutanen da suke shan azumi da gangan ba tare da wani uzuri a cikin alumarka.Don haka duk wanda ya ajiye azumi ba tare da wani uzuri karbabbe ba a sharia irin wannan azabar zaayi masa, saidai idan Allah ya azurta mutum da tuba. Domin wanda ya tuba na gaskiya, Allah zai karbi tubansa. Don haka masu irin wanna halayyar na shan azumi da gangan su daina. Kuma su sani cewa wannan azumin yana kansu, sai sun rama shi, Allah ya kiyaye mu.

SHEIKH JA’AFAR MAHMUD ADAM

No comments:

Post a Comment