Saturday, 12 January 2019

Yadda Ake Tuka Mota Idan Ana Ruwan Sama


Tuƙa mota a cikin ruwa yana da ban tsoro da kuma hatsari sosai. Saboda haka yana da kyau ka dau matakai domin gujewa hatsari a kan titi.

Mataki na ɗaya
Ka tabbatar ka wanke gilasan motarka sosai kar ka dinga barinsu da datti a jiki. Gani ta gilasai yana da muhimmanci sosai idan kana tuƙi, musamman idan ana ruwan sama. Saboda haka ka wanke ciki da wajen gilasan. Idan gilasan sunyi hazo-hazo ta ciki, sai ka kunnan AC a cikin motar.

Mataki na biyu
Kula da hasken motar. Zak iya kai motarka wajen gyara domin a saita maka fitulin motar su dinga haske yadda ya kamata da kuma haska wajen daya kamata. Idan kuma akwai fitilar da bata aiki sai kayi himmar chanzawa. Ƙura tana rage hasken fitilar mota idan ta taru a ciki, saboda haka a kiyaye.

Mataki na uku
Kula da tayar motar. Ramukan jikin taya (tiredi) sune suke sawa taya ta kama titi sosai, saboda haka a guji tafiya da tayar da ta siɗe musamman idan titin yana da santsi.

Sababbin tayoyi suna da kusan inchi 10/32 na tiredi. Dole ne a chanza taya a lokacin da tiredi yakai inchi 4/32. Taya da inchi 2/32 na tiredi bai kamata ayi amfani dasu a jikin mota ba ko kaɗan.

Mataki 4
Kunna wipers na jikin motar idan ana ruwan sama. Yana da kyau ka dinga chanza wipers ɗin motarka a ƙalla bayan shekara ɗaya domin kar su dinga baka matsala a lokutan da kake buƙatar su.
Mataki na 5
Rege gudu. A lokacin kowane yanayi mai haɗari ko yanayi mara kyau, abu na farko daya kamata kayi shine ka rage gudun da kake yi a cikin moatar. Titi da yake da santsi yana rage tsayuwar tayarka a jikin titin da kusan kaso ɗaya cikin uku. Saboda haka, kaima sai ka rage gudun ka da kaso ɗaya bisa uku. Haka zalika, idan titi yana da santsi, to zakaga baka da iko sosai akan birkin motar.

Mataki na 6
Ci gaba da mayar da hankali. Idan ba kaine kake tuƙa motar ba, yana da kyau ka taya direban wajen duba titi sosai domin gujewa motoci da kuma masu tafiya a ƙasa, musannan idan ana ruwan sama. Domin ka ƙara mayar da hankali, zaka iya kashe akwatin radiyon cikin motar ko kuma doguwar hira da akeyi da mutanen cikin motar. Haka zalika ciye-ciye a cikin mota ya kamata ya tsaya.

Mataki na 7
A kunna haske. A lokacin da aka fara ruwan sama, kaima sai ka kunna fitulun motar ko da kuwa da rana ne. Yin tuƙi ba tare da kunnan fitulu ba haramun ne a wasu ƙasashen duniya idan ana ruwan sama. Kunnan hasken motarka yana sawa sauran masu tuƙi su ankara dakai, sannan kuma idan ana ruwa gari yana yin duhu, saboda haka kunnan fitala zai taimaka sosai.

Mataki na 8
Yin tuƙi da hannu biyu akan sitiyari. Hakan zai baka damar samun iko akan motarka idan wani abu da ba’a so ya faru. Idan zak iya saka hannayenka, ɗaya yana kallon karfe 9 na hannun agogo ɗayan kuma yana kallon karfe 3 na hannun agogo to lallai zaka samu iko sosai akan sitiyarin motar.

Mataki na 9
Ka bada tazara tsakanin motar gabanka. Idan zaka iya bada tazarar misali sakanni biyar tsakanin ka da motar gabanka to zai taimaka maka idan an samu matsala da motar gaban naka.

Mataki na 10
Ka guji danna birki da ƙarfi. Dannan birkin mota da ƙarfi musamman idan ana ruwan sama, zaisa ka fada gaba sannan haka zalika zai sa ruwan ya shiga cikin birkin ka, don haka su rage aiki sosai. Maimakon ka taka birki lokaci ɗaya, zaka iya ɗauke ƙafarka daga kan totir domin ka rage gudu.

Mataki na 11
A sha kwana a hankali. San kwana da gudu idan titi yana da santsi zai iya sawa ka kasa riƙe motar sosai.  Yawancin kwanoni suna da sayn bod domin ya nuna maka. Kamar yadda akayi bayanin tuƙi, itama shan wana yana da kyau ka rage gudun ka zuwa ɗaya bisa uku.

Mataki na 12
Kada kayi amfani da ‘cruise’. shi wannan wajen idan ka danna, to motar zata dinga tafiya ne da kanta da gudu daya.

Mataki na 13
Ka tsaya idan hakan zai fi. Kar ka taɓa jin tsoro ko shayin tsayawa a gama ruwan sama idan kana ganin matsala zata iya faruwa.No comments:

Post a Comment