Saturday, 12 January 2019

Yadda Ake Siyan Data Me Sauki Daga MTN


Shin kana tinanin wace data zaka siya daga wajen MTN ne? A wannan lokacin zamuyi magana akan yadda zaka siyi data daga mtn da kuma kudin ko wacce data. Kowa yasan mtn shine kamfanin kira mafi girma a Nigeria gaba daya, domin kuwa bincike yanuna cewa a cikin duk mutane goma to mutane shida suna anfani da mtn.

Akwai data kala-kala daga mtn wadanda suka hada daga ta rana daya, sati daya, wata daya dama wadda tafi haka. Kafin ka sayi data daga mtn yana da kyau kayi hasashen abinda zakayi da datar da kuma kwanakin da kake so ta dade.

Amma idan bakasan siyan data, zaka iya amfani da tsarin mtn wanda zaka dinga biyan kwabo biyar a duk kilobyte daya. A hakikanin gaskiya wannan tasarin yana da tsada sosai.

Data ta kwana daya
* Domin siyan 50mb na kwana daya sai a tura 104 zuwa 131 ta sako. Ko kuma a danna *131*1*1*1#. zasu ciri naira dari (N100). yawancin muatne suna amfani da wannan ne idan suna son gwada karfin gudun network a inda suke ko kuma mutum yana son duba abu yanzu yanzu kuma babu kudi da yawa a wajensa.
* Domin siyan 150mb na kwan daya sai a tura 113 zuwa 131. zasu ciri naira dari biyu (N200).
Data ta sati daya.
* domin siyan 150mb na sati day sai a tura 102 zuwa 131. zasu ciri naira dari uku (N300).
* Domin siyan 500MB da kiuma kyautar 250MB na sati daya sai a tura 103 zuwa 131. Zasu ciri naira dari uku (N500)

Data ta wata daya:
* Domin siyan 1GB da kuma kyautar 500MB na wata daya sai a tura 106 zuwa 131. Zasu ciri naira dubu daya (N1000).
* Domin siyan 1.5GB sai a tura 130 zuwa 131. Zasu cire naira dubu daya da dari biyu (N1200)
* Domin siyan 2GB na wata daya sai a tura 110 zuwa 131. Zasu ciri naira dubu biyu (N2000) sannan zasu baka 2.5GB da kuma 1GB kyauta.
* Domin siyan 5GB na wata daya sai a tura 107 zuwa 131. zasu ciri naira dubu uku da dari biyar (N3500).
* Domin siyan 10GB na wata daya sai a tura 116 zuwa 131. zasu ciri naira dubu biyar (N5,000).
* Domin siyan 22GB na wata daya sai a tura 117 zuwa 131. zasu ciri naira dubu goma (N10,000).

Data ta watanni biyu
* Domin siyan 50GB na watnni biyu sai a tura 118 zuwa 131. zasu ciri naira dubu ashirin (N20,000).

Data ta watanni uku
* Domin siyan 85GB na watanni uku sai a tura 133 zuwa 131. zasu ciri naira dubu hamsin (N50,000).
- A lura da cewa idan ka siyi data sannan suka baka karin bonus akan datar to wannan bonus din zaka iya amfani dashi ne daga karfe daya na dare zuwa bakwai na safe.
- domin ka sayi wadannan datar dana ambata a baya a saukake sai ka danna *131#.No comments:

Post a Comment