Tuesday, 22 January 2019

Yadda Ake Sawa Jariri Yayi Bacci

Kula da jariri sabuwar haiwuwa yana da wahala sosai musamman idan yin bacci yana yi masa wahala. Sannan wasu mutanen suna so su dinga sa jariransu su dinga bacci a lokacin da suke so. Akwai hanyoyi da idan mukayi amfani dasu zamu iya sawa jariranmu su dinga bacci a lokacin da muke bukata.


1. A dinga chanza masa pampers ko napkin. Idan kinsan cewa jaririnki ya bata pampers din da kika saka masa, yana da kyau ki chanza masa wani, idan ma napkin kika yi masa shima sai a chanza masa. Dalili kuwa shine, idan pampers din ya baci, yana takurwa yaron wanda zai iya jawowa ya hana shi bacci.

Haka zalika, idan kika saka masa kaya wanda baya jin dadin su, suma zasu iyta hana shi yin bacci. Misali, idan zafi akeyi, ki saka masa kaya marasa nauyi, idan kuma sanyi akeyi sai ki saka masa kaya masu nauyi domin yaji dumi sosai.

Bincike ya nuna cewa yawancin jarirai sababbin haiwuwa ana chanza musu pampers kamar sau biyu zuwa uku a rana, sannan idan suna kara girama yawan bata pampers din yana karuwa zuwa biyar ko shida.

2. A bawa jaririn abinci. Akwai lokutan da jararin baya samun bacci saboda yana jin yunwa. Saboda haka a dinga bawa jariri abinci akan kari domin ya dinga bacci a lokacin dsa yake so. Amma ki sani cewa jarirai basa iya yin bacci ba har safiya ta waye ba tare da sun sha nono ba.

Bincike ya nuna cewa jarari suna shan nono a kalla buk bayan awanni biyu zuwa uku amma kuma idan madarar jarirai ake basu, a kalla duk bayan awanni biyu ko uku.3. Ki jijjiga yaron idan yana kuka. Idan yaro yana kuka yana da kyau ki dauke shi domin kin jijjiga shi, idan kuma ya daina kuka yana da kyau ki rungume shi domin yayi bacci. Ki gane cewa nunawa yara soyayya mai yawa yana iya lalata tarbiyyar su, amma idan jariri ne nuna masa soyayya bata lalata shi. Saboda haka a nuna masa soyayya yadda ya kamata.

4. A dinga duba fatar jaririn domin jin sanyi ko zafi. Yana da kyau ki dinga agne lokacin da jaririnki yake jin sanyi ko zafi domin ki dauki matakin daya dace. Idan kika ga yana jin zafi ko yana gumi, yana da kyau ki rage yawan kayan da yake jikinsa. Idan kuma kika ga alamar sanyi yake ji, sai ki kara masa kayan sanyi.

5. A lura da alamomin jin bacci daga jaririn. Akwai alamomin da yawancin jarirai suke nunawa idan suna so suyi bacci. Saboda ahaka, idan akaga wadannan alamomin yana da kyau a kwantar dasu domin wannan ne lokacin da zasuyi bacci. Wasu daga cikin alamomin sun hada da, yin kuka, murza idanu da kuma jan kunnensu.

6. A kwantar dashi akan gadonsa. Idan akaga alamomin jin bacci amma kuma baiyi baccin ba, yana da kyau a kwantar dashi domin yayi baccin. Amma kafin ayi hakan, yana da kyau a bashi nono sannan kuma chanza masa pampers idan ya bata domin ya samu yayi bacci mai dadi.7. A kwantar dashi akan bayansa. Idan za’a kwantyar da jariri, yana da kyau a kwantar dashi akan bayansa. Kar a dinga kwantar da jariri akan cikinsa ko kuma a gefen hannunsa. Bugu da kari kuma, a dinga cire duk wasu manyan kayan wasa daga cikin gadon nasa domin baya bukatar su sannan kuma zasu iya hana shi shan iska ta hancinsa. Kar a dinga barin jariri yayi kusa sama da minti daya ba tare da anje an dauke shi ba.

8. A kunnan haske da rana, da dare kuma a rage haske. Idan ana so yaro yai bacci da rana, yana da kyau a bude labule domin haske ya shigo, idan kuma dare ne sai a bar haske kadan daga fitala. Sannan idan zaiyi baccin rana shima a rage haske. A guji yin magana ko wasanni idan jariri yana bacci domin hakan zai tashe shi kuma yasa komawarsa baccin yayi wahala.

9. A barshi yayi bacci idan yana bukata. Mun sani cewa ida mutum yayi bacci mai yawa da rana, bacci da dare yana yi masa wahala. Amma wannan bayay faruwa akan jarirai. Saboda haka a barshi yayi bacci lokacin dayake so sannan kuma kar a tilasta masa yayi bacci. Bincike ya nuna cewa jirirar suna bacci a kalla awanni goma sha tara a cikin awanni ashirin da hudu.

Shawara ta anan shine, idan yaranki yana bacci da rana, kema ki samu kiyi bacci a wannan lokacin idan zaki iya domin idan dare yayi ki samu ki lura dashi.

10. A dinga karanta masa labari kafin ya kwanta. Idan kina san yaranki ya tashi a rauwar turawa, sai ki dinga karanta masa littafi duk da cewa baya agne abinda kike fada masa har ya fara girma ya gane cewa idan ana karanta littafi to lokacin bacci yayi.No comments:

Post a Comment