Tuesday, 29 January 2019

Yadda ake rubuta wasikar soyayyaYawancin mutane yanzu sunfi amfani da sakonni na waya (text message) ko kuma sakonni na E-mail wajen tura sakonninsu. Amma kuma kar ku manta akwai wata hanya ta ruba sako wadda ta dade kuma take musamman idan aka rubuta ta da hannu. 
Mutane suna daukar irin wannan sakon soyayyar da muhimmanci musamman ganin cewa mutane baa amfani dashia sosai a wannan zamanin. Rubuta wasikar soyayya ba abu bane mai wahala, amma kuma yana bukatar kasan yadda zakayi ka bayyana soyayyar taka/ki.
Mataki na daya: shirin rubuta wasikar

1. Ka shiga cikin yanayi. Idan kana son rubuta wasikar soyayya, yana da kyau ka samu waje na sirri wanda babu wanda zai dame ka ko ya takura maka. Zaka iya kunna wani sauti wanda zai shigar da kai cikin yanayin soyayya idan kana son yin hakan. Idan ma zaka iya dauko hoton masoyiyar taka ko masoyin naki domin ki dinga kalla, zaka/ki iya yin hakan.

2. Ka tina lokacin matukar soyayya. Akwai lokutan da zakaji ka shiga cikin kogin soyayya tsundum. To irin wannan lokacin zaka tina domin ya taimaka maka wajen rubuta kalaman soyayya masu armashi.

3. Kayi tiananin wadda kake so din. Galibi idan kuka fara soyayya akwai abinda ka gani a gareta wanda ya dauki hankalinka har ka fara santa kuma ya dawwamar da kai a soyayyar. Misali, tana da kyau, kira, wanka, iya magana, dabi’a, iya magana da sauransu. Ka fada mata duk wadannan abubuwan domin ta gane cewa kaga tana dasu kuma ka yaba mata akan hakan. Ka rubuta wadannan abubuwan a gefe sannan ka dauke su dya bayan daya kana rubutu a kansu. Misali
- ina san yadda kike kallo na da nufin kina so na
- Ina jin dadin yadda kike da hali mai kyau.
- Ina godiya da karfafa min gwiwa da kike idan matsala ta faru.
- Murmushinki guda daya yana cikani da farin ciki kullum.

Kar ka dinga rubutu kawai akan yadda kirar jikinta yake, ka dinga hadawa da halayyarta. Amma kuma kar wai kaki rubuta komai akan yadda kirar ta take domin kuwa tana san jin ace ta hadu.

4. Ka tina yanayin da kuke ku biyu na farin ciki. Akwai lokutan farin ciki da ku biyu ne kuka sani. Ka dinga tina wannan lokaci kana rubuta mata shi a cikin wasikar. Misali, zaka iya fada mata lokacinda ka fara ganinta ko kuma lokacin da ka ganta kake son yi mata magana tun daga kayan jiknka da yadda kaji shakkar zuwa ka sameta. Ka rubuta mata duka abubuwan da zaka iya tinawa.

5. Kayi tinanin nan gaba. Dyk da cewa soyayyar ku tana da abaya, tabbas akwai abubuwan da kuke so su faru nan gaba. Idan bakwa tare kayi mata bayanin abubuwan da zakuyi idan Allah ya hada ku. Idan ka kasance baka da lokaci ne, kayi mata bayanin irin abubuwan da kake shirya muku da wannan lokacin naka.

6. Ka dauki wannan a matsayin ranar karshenka ce a duniya. Kar kaji kunya, kayi rubutu kamar kai soja ne kana filin yaki, kar kaji kunyar fada mata duk abinda kake son fada mata a baya.

Mataki na biyu: Rubuta wasikar

7. Ka rubuta wasikar gwaji. Ka sami takarda wadda zaka fara rubuta wasikar daga baya kuma ka kwafe ta zuwa ainihin takardar wasikar taka. Kar ka damu da tangarda da zaka samu a wannan rubutun saboda zaka gyara shi idan kazo rubuta ainihin wasikar. Abu mafi muhimmanci shine gundarin sakon da kake so ka rubuta.

Ka dauki lokacinka, kar ka dinga sauri wajen rubuta wasikar sannan kuma idan wannan ce wasikar ka ta farko ka gane cewa zaka iya yin kuskure a ciki saboda haka kar ka damu.

Ka gane irin soyayyar da kuke, irin kalaman da zaka fadawa matarka ta sure bayan shekara ashirin da aurenku daban yake da irin wanda zaka fada mata idan kuna saurayi da budurwa. Sannan kar ka manta ka fada mata kana santa a kalla sau daya a takardar.

8. Ka fara bude rubutun wasikar. Ka fara da fada mata dalilin rubuta wasikar, ka nuna mata wasikar soyayya ce tun a farkon takardar. Zaka iya ce mata “ina yawan tinaninki soai a kwanakin nan saboda haka ina san nuna miki yadda kike da muhimmanci a rayuwata”. ka fadi ra’yainka kar ka dinga boye-boye

9. Ka rubuta gangar jikin wasikar. A wannan lokacin ne zaka nuna ainihin yadda kake san nata, duk wani lokacin farin ciki. Zaka fada mata yadda kake sonta, dalilin dayasa kake santa yadda kake ji idan kana tare dasu, yadda ta chanza maka rayuwa bayan kun hadu da kuma yadda rayuwa zata kasance idan babu ita.

Yawanci ana rubuta wasikar soyayya ne domin ka fadi wasu abubuwan da baka iya fadarsu a fili. Saboda haka kayi amfani da duk wani sal na nuna soyayya a wannan lokacin. Kayi amfani da abubuwan da ka rubuta a fari domin su taimaka maka.

10. Ka rubuta alheri. Kar ka dinga rubuta sharri ko kuma wani abu da akeyi ba dai-dai ba. Ka tina cewa yaran da zaka haifa zasu iya riskar wannan wasikar. Ka ka kuskura ka rubuta aibunta ko guda daya a cikin wasikar.

Misali, idan zaka rubutawa matarka wasika, zaka iya cewa fada mata cewa har yanzu kana jin shaukin soyayya duk lokacin da tayi maka murmushi duk da cewa kuwa kun shekara goma da aure. Ko kuma kace mata kana santa sama da yadda kake santa a baya.

11. Ka nuna mata ma’anar har abada. Muna son soyayyar mu taci gaba da dorewa, sabod haka ka nuna mata yadda kae so ku kasance a nan gaba cewa babu abinda zai shiga tsakanin soyayyarku sai mutuwa.

12. Ka rufe takardar taka. Yana da kyau a karshen takardar ma ka nuna soyayya. Misali zaka iya rufe takardar da cewa “ina sa ran nayi mafarkinki yau” ko kuma “Na kagu na kare rayuwa ta dake acikinta”.

Mataki na uku: kammala wasikar

13. Ka sami takarda. Bayan ka gama rubuta wasikar, sai ka sami takarda mai kayu bawai jigari-jigari ba. Zaka iya samun mai dan tsada wadda duk wanda ya gani yasan wanann mai muhimmanci ce. Zaka iya yin rubuta akan takardar littafi idan baka da mai tsada ko kuma ma ka hada takardarka, idan kuma da hali sai ka mayar da takardar ta koma tsohuwa.

Kayi amfani da bakin biro ko kuma ruwan kasa. Ka guki amfani da birukan malamai kamar shudi, kore ko kuma ja. Domin kuwa rubutun ka zai zamo kamar ka rubuta aikin gida ne.

14. Rubuta sunan wanda ake so. Zaka iya rubuta zuwa ga ‘abin kauna’ ko ‘masoyiya’ ko ‘rabin rai’ ko ‘mafi kyau’. Sannan zaka iya rubuta zuwa ga ‘Masoyiyata’ ko ‘abin kauna ta’. amma fa idan kana san nuna soyayyarka ne a karin fari, kar kayi amfani da wadannan kalaman, kawa ka rubuta zuwa ga abin kaunar kowa.

15. Ka rubuta kwanan wata. Ka rubuta kwanan wata domin tarihi ya tina. Za’a dinga karanta wasikar lokaci-bayan lokaci saboda haka duk lokacin da aka duba kwanan wata kara dankon soyayya yakeyi.

16. Ka kara rubuta wasikar. Ka dauko wannan takardar da zaka bata domin ka kwafe duk abubuwan da ka rubuta a takardar gwaji, sannan kuma kayi gyare-gyare a wuraren da kaga suna bukatar gyara. Ka tsaftace rubutun naka kar ka bari takardar tayi datti.

17. Ka rufe waikar da kalamai. Zaka iya amfani da Love always, Soyayya koda yaushe, Forever yours da sauransu.

18. Ka karawa takardar armashi. Zaka iya fesa mata turare ko kuma ka hada da flower mai kamshi. Da dai sauran abubuwan da zasu karawa takardar armashi.

19. A saka wasikar a ambulan (envelope). bayan ka gama abubuwan dana ambata a baya, sai ka ninke takardar ka sami ambulan daya dace da takardar sannan ka saka ta a ciki. Idan kuma baka son hakan, sai ka nannade takardar sannan ka samu zare ka daure ta dashi.

20. Ka bata mamaki. Zaka iya tura wasikar ta hanyar post office domin tasha mamaki sosai domin bamu saba yin hakan ba. Idan kuma matarka ce zaka iya boye takardar a kasan pillow dinta na kwanciya ko a cikin kwabar kayanta. Zama ka iya sakawa plate na abinci ka kawo sai ta bude taga wasika ce.

Zaka iya dan jinkirtawa kadan kafin ka bada takardar domin ka tabbatar babu matsala ko kuma wani abu da zakayi danasinshi nan gaba

 21. Daga karshe. Kar a zata dan ina amfani da jinsin namiji a rubutun nan ina nufin maza ne kawai zasu iya amfani da wannan darashin. Mata ma zasu amfani dashi wajen rubutawa masoyansu da mazajen aurensu.


A takaice
Idan za’a rubuta wasikar soyayya sai a lura da wadannan abubuwan:
- Ka shiga cikin yanayi. 
- Ka tina lokacin matukar soyayya.
- Kayi tiananin wadda kake so din.
- Ka tina yanayin da kuke ku biyu na farin ciki.
- Kayi tinanin nan gaba.
- Ka dauki wannan a matsayin ranar karshenka ce a duniya.
- Ka rubuta wasikar gwaji.
- Ka fara bude rubutun wasikar.
- Ka rubuta gangar jikin wasikar.
- Ka rubuta alheri.
- Ka nuna mata ma’anar har abada.
- Ka rufe takardar taka.
- Ka sami takarda.
- Rubuta sunan wanda ake so.
- Ka rubuta kwanan wata.
- Ka kara rubuta wasikar.
- Ka rufe waikar da kalamai.
- Ka karawa takardar armashi.
- A saka wasikar a ambulan (envelope).
- Ka bata mamaki.
- Daga karshe.

No comments:

Post a Comment