Friday, 18 January 2019

Yadda ake miyar waken suya

Abubuwan da kae bukata:
- Nama
- Kifi
- kayan miya
- Waken suya
- Maggi
- Gishiri
- kayan kamshi
Yadda ake hadawa:
Da farko za ki gyara Waken suya sai a soyashi a kasko sannan a niko a kuma tankade sai a dafa Nama idan ya dahu sa a sauke daga nan sai a zuba manja a tukunya tare da albasa ta soyu sannan sai a zuba markadedden kayan miya a ciki idan ya fara soyuwa sai a kawo tafasasshen Naman a zuba a ciki tare da gyarerren busasshen Kifi a zuba Maggi, Gishiri, Curry da Tafarnuwa (ga mai so). idan suka soyu sai a dauko ruwan naman nan a zuba a ciki tare da garin waken sauyar nan sai bayan ta juya sai ta barshi ya dahu, idan ya kusan dahuwa sai ta wanke yankakken alaiyahunta ta zuba idan ya yi kamar minti uku zuwa biyar sai ta sauke. Ana iya cin wannan miyar da tuwon shinkafa. 

No comments:

Post a Comment