Thursday, 17 January 2019

Yadda Ake Hada Hirar karya A WhatsApp (Fake Chat)


A wannan duniyar tamu da chatting ya zama daya daga cikin abunda mukeyi kullum, yana da kyau mu koyi yadda ake yin abubuwa dban-daban da wayar mu ta Android. Dayawa zamu iya ganin hotunan hira ta ban dariya a yanar gizo, amma yawancin wadannan hotunan hirar bana gaskiya bane, an hada su ne kawai domin nishadi ko kuma wata manufa. Saboda haka, a wannan lokacin zamu koya muku yadda zaku dinga hada hira wadda bakuyi ba kuma ta zama ta gaske ba tare da kunce abokinku yayi muku maganar da kuke so ba ko kuma kunyi amfani da application na gyara hotuna.

Amma kafin mufara, muna koyar da wannan dabarar ne domin ilimi kawai. Kar wani yayi amfani da hakan wajen bata wa wani rai ko kuma amfani dashi ta hanyar da bai dace ba.

Abun nishadi shine zaka iya rubuta sunan mutumin da kake so, zaka iya saka masa hoto (DP) da kake so, karshen hawansa (Last Seen) da sauransu. Akwai application masu yawa da zamu iya amfani dasu domin yin wadannan abubuwan. Amma a wannan lokacin zamuyi magana ne akan guda biyu da suka fi shahara.Na daya: Yazzy App

Yazzy daya daga cikin application ne da ake amfani dasu wajen hada hira ta karya. Bugu da kari, shine application na daya a duniya da mutane sukafi amfani dashi wajen yin wannan aikin.
- Ka shiga Google Play Store a wayar ka.
- Sai ka rubuta Yazzy app
- Sai ka danna download domin ka dauko application din zuwa wayarka.
- Za zarar ka dauko shi sai kabi wadannan matakan:

1. Ka bude application din sai ka danna New WhatsApp. Zakaga wani shafi ya bude irin wannan na kasa.

2. Idan zaka chanza wa masa suna sai ka danna kan Name
3. Idan zaka chanza masa hoto (DP) sai ka danna wajen da hoton yake
4. Idan zaka cire yazzy da aka rubuta a kasa, shima sai ka danna akansa.
5. Idan zaka chanza hoton bangon hirar (Background Image) shima sai ka danna digo guda uku dake saman shafin daga kusurwar dama. Sai ka danna Change Backgroung. Daga nan kuma sai ka saka hoton da kake so.
6. Akwai wani abu a kasan shafin mai ruwan kasa, an rubuta + a jikinsa. Shi wanna yana da muhimmanci sosai, domin da shine zaka tura sabon sako, da shi ne zaka turowa kan ka sako sannan da shine zaka tura hotuna ko ka tura wa kanka. Da dai sauransu.

7. Bayan ka gama saita komai, ka tura sakonnin kamar yadda ranka yake so, sai ka dannan Save sannan ka tura wanda kake so ya gani.
8. Bugu da kari zaka iya hada hira ta group da wannan application din.
Na biyu: Prank

Shima wannan application din a Google play store zaka dauko shi. Bayan ya shigo wayarka sai ka fara chanza sunan abubuwan da kake so yadda kake bukatar su kasance kamar suna, DP, hoto, hira da sauransu.Bayan ka gama komai sai kayi screen shot domin ka turawa abokanan ka.

A takaice:
Idan kai me ban dariya ne a yanar gizo zaka iya amfani da wadannan hanyoyin domin ka dinga hada hora ta ban dariya. Amma ku sani cewa wannan hanyoyin sun halatta ayi amfani dasu a duniyar yanar gizo. Amma idan kayi amfani dasu ta hanyar da basu dace ba domin ka sawa wani bakin ciki, Allah ne zai yi maka hisabi. Idan kana da wani abu da kake son koya wa mutane zaka iya tuntubarmu domin mu baka dama.

Kar a manta ayi comment a kasan wannan post din.

No comments:

Post a Comment