Saturday, 5 January 2019

Yadda Ake Ganewa Idan an Katangeka (blocking) Dinka a WhatsApp


Idan kana fuskantar wahala wajen tuntuɓar wani a kan shafin sadarwa na WhatsApp, zai iya yiwuwa mutumin ya katange ka ne. Amma fa ka sani cewa kanfanin WhatsApp bazi faɗa maka idan wani ya katange ka ba.

Matakai

Mataki na ɗaya
Bude WhatsApp.

Mataki na biyu
Shiga "Contacts" wato Lambobin sadarwa.

Mataki na uku
Gungura zuwa sunan wanda kake tinanin ya katange ka.

Mataki na huɗu
Sai ka danna akan sunan. Daga nan sai ka nemo matsayin mutumin wato ‘last seen’. Idan babu matsayi, kamar "online" ko "last seen," ya bayyana a ƙarƙashin sunan mai lambar, to zai iya yiwuwa ya katange ka.

Mataki na biyar
Duba hoto. Yawanci idan mutum ya katange ka, zakaga ka daina ganin hotonsa wato ‘profile picture’.
Mataki na shida
Tura saƙo. Idan ka tura masa saƙo zakaga alamar tafiyar saƙo guda daya ne zai fito har bayan kwanaki da yawa. Amma idan alamar ta zama guda biyu kenan saƙon ya shiga, ba’a katange ka ba.

Mataki na bakwai
Duba ‘Profile’. zaka baka ganin abinda ya rubuta a status nasa wanda yake fitowa a ƙasan lambarsa.

Mataki na takwas
Kammala bincikenka. Idan kaga alamu kamar guda biyu da aka ambata a baya, sai ka fara tinanin an katange ka ne.

No comments:

Post a Comment