Wednesday, 16 January 2019

Yadda Ake Dauko Bidiyo Daga Instagram (A Saukake)


Idan kan cikin instagram kuma kaga wani biyo daya birgika, zaka iya dauko shi zuwa cikin wayarka a saukake idan kabi wadannan hanyoyin da zan bayyana.
1. Kayi amfani da application mai suna ‘GbInstagram’

- Ka shiga cikin browser (Google Chrome)
- Ka rubuta ‘Download Gb Instagram’
- Sai ka shiga cikin daya daga cikin sakamakon da zasu kawo maka.
- Sai kayi installing bayan ya shigo wayarka.
- Sai ka shiga cikin application din ta hanyar saka sunanka da kuma lambar tsaroi.
- Sai kaje shafin da bidiyon yake.
- Sai ka danna digo guda uke dake saman bidiyon.

- Sai ka danna GB options.

- Sai ka danna Download

- Shikenan zai shigo wayarka.

2. Kayi amfani da application me suna ‘Video Downloader for Instagram’
Idan kana bukatar wannan application din

- Zaka shiga ‘Google Play Store.
- Sai ka shiga wajen nema (Searching).
- sai ka rubuta Video download for instagram.
- Sai ka shiga dauko wanda zasu kawo maka.
- Sai ka shiga Instaram bayan ka gama.
- Sai kaje kan bidiyon da kake so ka dauko.
- Sai ka danna digo guda ukun dake saman bidiyon.
- Sai ka danna ‘Copy Link’
- Sai ka koma kan sabon application din da ka dauko daga Play Store.
- Sai ka danna ‘Allow’ idan ta tambayeka.
- Sai ka rubuta wannan adireshin daka kwafa. Amma wani lokacin zai bude maka da kansa ne.
- Sai ka danna ‘SHARE’.
- Sai ka danna ‘Download Image’ (amma idan an kawo maka talla, zaka iya danna X dake saman tallan.
- Shikenan bidiyon zai shigo wayarka.

3. Kayi amfani da shafin yanar gizo me suna ‘SaveFrom’
- Ka bude Instaram.
- Sai kaje kan bidiyon da kake so ka dauko.
- Sai ka danna digo guda ukun dake saman bidiyon.
- Sai ka danna ‘Copy Link’.
- Sai ka shiga browser ta cikin wayarka (Google Chrome).
- Sai ka shiga wajen da ake rubuta adireshi.
- Sai ka rubuta savefrom.net domin ta bude maka shafin.
- Sai ka shiga wajen da ake neman domin ka rubuta wannan adireshin da ka kwafo daga Instagram. (ta hanyar pasting)
- Sai ka danna download.
- Zai bude sabon shafi, sai ka kara danna download.
- shikenan zai shigo wayarka.3 comments: