Saturday, 12 January 2019

Yadda Ake Dambu Kala Kala guda 12


Na ɗaya: Dambun shinkafa

Abubuwan da kike buƙata
Shinkafa (Rice)
Karas (Carrot)
Koren tattasai (Green pepper)
Kabeji (Cabbage)
Man ƙuki (Ground-nut Oil)
Maggi
Kori (Curry)
Spices ...

Matakai:
Za'a ɓarza shinkafa a injin da ake barje. Bayan nan sai a tankaɗe tsakin shinkafar da rariya. Sai a ajiye a gafe.
Sai a samo ruwan ruwan zafi a wanke shinkafar da aka tankaɗe. Idan ya ɗanyi laushi kaɗan sai a tsane da matsami. Bayan ya gama tsanewa ne sai ajuye shi a roba mai faɗi.
Bayan nan sai a yayyanka kabeji, a gurza karas, a yanka koren tattasai duk a zuba su a cikin robar. A saka man ƙuli kaɗan, a zuba maggi, curry, spices, da ɗan gishiri kaɗan, agarwaya su tare har sai sun haɗu sosai.

A zuba haɗin a cikin leda mai kyau a saka a madambacci atoshe ko ina sai arufe adora a wuta.
Idan yayi za'aji ya fara qamshi. Sai a sauke a ƙara man ƙuli idan ana buƙata. A zuba a ci da ɗuminsa.
Na biyu: Dambun kuskus

Abubuwan da ake buƙata:
Kus-kus (Couscous)
Karas (Carrot)
Niƙaƙƙen Nama (grinded meat)
Alayyahu
Man ƙuli (groundnut oil)
albasa (albasa)
Koren tattasai (Green pepper)
Attarugu
Curry
Maggi
Spices..

Matakai:
Za'a juye kus-kus ɗin a roba, ajuye niƙaƙƙen nama a kai, ayanka karas a kai, ayanka albasa da tarugu azuba a kai, sannan sai a yanka koren tattasai a sa a kai. Sai a juya har sai sun haɗu sosai.
Bayan nan sai a zuba mangyada yadda zai isa, a sa maggi, curry da spices aciki sannan a ƙara juyawa sosai
Sai a yanka alayyahu a sa a ciki, sannan agaurayasu, a dinga zubawa a cikin fararen leda ana ƙuƙƙullawa.
Bayan an gama sai a saka a cikin tukunya a turarashi kamar alale. Yafi daɗi idan aka ci shi da ɗuminsa.

Na uku: Dambun ACCA

Abubuwan da ake buƙata:
ACCA
Kara sa (Carrot)
Kabeji (Cabbage)
Kifi (fish)
albasa (albasa),
Koren tattasai (green pepper)
tarugu
Mai
Maggi, curry, spices..

Matakai:
A sami roba mai kyau sai azuba ACCA a ciki sannan a yayafa ma sa ruwan dumi kaɗan.
Sai a yanka kabeji ƙanana a zuba akan accan, a gurza karas, a yayyanka albasa, tarugu, da koren tattasai ƙananan yanka sai a zuba a kai.
A dafa/tafa sa kifi da kayan ƙamshi a marma sa kifin a kai sai a juya haɗin sosai
Bayan nan sai a sa man gyaɗa, maggi, curry, da spices a kai, sai a garwaya su. sannan azuba a madanbacci a turara.
Idan yayi zaifara qamshi. A ci da ɗuminsa.

Na huɗu: Dambun Alkama

Abubuwan da ake buƙata:
Alkama
Cabbage
Carrot
Zabuwa
Kore tattasai (G/pepper)
albasa da tarugu
Curry, maggi spices
Man gyaɗa

Matakai:
a samu alkama a ɓarzata a wanke da ruwan ɗumi a tsane a matsami, inya tsane, ajuye a roba, adafa zabuwa da kayan qanshi yadafu ligib, sai a ciccire tsokan naman a guggutsurashi azuba akan tsakin alkamar, ayanka kabejie da karas azuba a kai, ayanka albasa albasa, tarugu da koren tattasai a zuba a kai, a sa mai, a sa maggi, curry da spices aciki, sai a garwayasu a zuba a madanbacci a turara...
Na biyar: Dambun Tsakin Ma sara

Abubuwan da ake buƙata:
Tsakin ma sara
Rama
Gyaɗa
Kanwa
Man gyaɗa
Tafarnuwa
Gishiri
Ɗanyar citta
albasa
ƙarago
Kifi ( banda )

Matakai:
Za'a samu tsakin ma sara a wankeshi da ruwan ɗumi, sai a tsaneshi da matsami, idan ya tsane a juye a roba, a juye banda a roba a zuba ruwan zafi a kai, inyayi laushi a gutsutsura bandan a kan tsakin, sai a daka gyada a zuba a kai, adafa Rama sama sama a zuba a kai, a sa ruwan kanwa kaɗan a kai, abarbaɗa garin tafarnuwa kaɗan, ayanka ɗanyar citta a zuba a ciki, a sa man gyaɗa yadda zai isa, a sa gishiri kaɗan, a sa maggi da ajino aciki, a sa curry da spices, sai a garwaya a zuba a madanbacci a turara, idan yayi a sauke azuba garin ƙarago da mai kaɗan

Na shida: Dambun Zogale

Abubuwan da ake buƙata:
Zogale
kuskus
Kifi
albasa, tarugu
Koren tattasai (Green pepper)
Man gyaɗa
Curry, maggi da spices..

Matakai:
Adafa zogale sama sama sai a tsane a matsami, inya tsane, a kawo kus-kus ajuye a kai, a kawo sardine fish a marma sa a kai, a yayyanka albasa da tarugu a kai, a sa mai, curry, maggi & spices a kai, sai a garwaya, a dinga zubawa a fararen leda ana ƙullawa, a turarashi kamar alale

Na bakwai: DANBUM DANKALI

Abubuwan da ake buƙata
Tumatur
ƙwai
Gishiri
Magi
Kori
Dankali
Albasa

Matakai:
Za'a feraye dankali a soya amma kada ya soyu sosai, idan ya ɗauko soyuwa sai a ɗauko ƙwai, tumatur da albasa. To dama an riga an yayyan ka kasu, sai a zuba a kan dankalin. Sai a dinga juyawa yana dagargajewa idan kwan ya soma yin yellow sai a sauke.
misali:- Dankali goma albasa biyu tumatur huɗu kwai uku.

Na takwas: DAMBUN KIFI

Abubuwan da ake buƙata:
Kifi
Maggi
Gishiri & curry
Attarugu
Albasa

Matakai:
Ki gyara kifinki ki tafasa ki cire ƙaya ki watse kifin kizuba maggi, curry, albasa da tarugu.
Sai ki aza a saman wuta ki soya shima idan ya fara watsewa toh ya soyu shikenan sai kikwashe.

Na tara: (DAMBUN NAMA)

Abubwan da ake buƙata:
1-Nama
2-attaruhu da albasa
3-Maggi
4-citta
5-mai
6-turmi
7-kaskon suya
    
Matakai:
Da farko zaki sami namanki mai kyau mara kashi da kitse se ki wanke ki zuba a tunkaya ki sa albasa da citta da maggi sai ki barshi yayi ta dahuwa. Idan ya dahu sae ki sauke ki kirba tare da attaruhu da albasa sai ki na ƙara maggi da onga in ya kirbu sosai sai ki zuba shi a kasko ko tukunya. Ki saka mai sosai ki soya, idan ya soyu ki kwashe zaki iya sa hannunki ki danna idan bakya san mai.

Na goma: DAMBUN NAMAN TUKUNYA
Shima haka zakiyi amma shi daga tafashen naman zaki dinga ƙara ruwa yana dahuwa daman kin haɗa attarugu da albasar gun dahuwar kinsa maggi da gishiri da citta sai ki ta ƙara ruwa har sai kinga ya farfashe sai kisa muciya ki bubbuga sai ya dagargaje sai ki zuba mai ki soya shikenan kingama.

Na goma sha ɗaya: DANBUN KUS-KUS

ABUBUWAN DA AKE BUKATA :-
Cous Cous
Nama/Hanta ko mince meat
Maggi
gishiri
Green beans
Albasa
attaruhu
zogale ko Alayyahu

YADDA ZAKI HADA :-
Ki tafasa nama ki sa ruwa da ɗan yawa, in ya dahu, ki yanka shi
ƙanana, duk kayan haɗinki ki yanka su ƙanana, sai ki juye ruwan
naman akan kus-kus, ki sa maggi, curry, gishiri ki juya sosai kisa
murfi ki barshi zuwa 5mnt,
Sai ki ɗauko madanbaci ki ɗora a wuta ki zuba kus-kus kisa leda ki rufe kamar yadda ake dambun tsaki, bayan mintuna biyar sai ki kwashe kus-kus ɗin kisa duk kayan haɗin da mai ki juya sosai ki Mayar a wuta zuwa mintuna uku ki sauke. zaki iya sa bawon kabeji. Yana da daɗi

Na goma sha biyu: Dambun naman kaza.

Abubuwan da ake buƙata
*kaza
*man gyaɗa
*kayan maggi
*kayan miya

Yadda akeyi:-
Zaki tafasa kazar ki da citta da maggi, sai albasa, in tayi laushi ki sauke ki soya sama-sama, saiki juye aroba ki cire tsokar, sai ki wanke kayan miya attarugu, tattasai, albasa ki jajjga a turmi, kisa maggi, curry, sannan ki juye naman ki daka duka. (karki manta ki fara soyawa sama-sama).
Idan ya daku ki juye a faranti ki barbazashi san nan ki sa mai a wuta ki rinka diba kaɗan kaɗan kina zubawa kina soyawa harki gama.No comments:

Post a Comment