Saturday, 5 January 2019

Yadda Ake Daina San Mutuminin da Kake So Amma Baya SankaSoyayya abace mai dadin gaske idan mutum yayai dace da wanda suke son juna tare. Amma idan aka sami akasin haka, wato bangare daya yana nuna soyayya amma daya bangaren baya mayar da soyayyar, matsala takan faru. Mutum a wannan yanayin zaiji kamar duniyar ma ta tashi kowa ma ya huta. Amma mu sani cewa zafin ciwon da mutum yake ji gaskiya ne domin kuwa binciken masana ya gano cewar idan kana son wanda baya sanka, hakan zai iya jawowa sinadaran jikin mutum da suke da alhakin jin ciwo/zafi/radadi su fara aiki sosai. Mu sani kuma cewa, mutum bashi da damar ya hana kanshi daina jin wannan ciwon amma kuma akwai hanyoyin da zasu rage maka radadin har ma kaji ka cigaba da rayuwa kamar yadda ka saba.

1. Kar ka zargi kanka. Idan kana san wani, shi kuma baya sanka to ka yarda da cewa wannan ciwon da zakaji a zuciyarka gaskiya ne domin kuwa gashi yana faruwa akanka. Kamar yadda na ambata a baya cewa masana sun gano cewa idan mutum ya nuna baya sanka zaka sami karin akan bugun da zuciyarka take. Yarda da cewa wannan ciwon da kake ji gaskiya ne zai taimka wajen ka fara neman hanyar magance matsalar. Domin kuwa akwai mutanen da basu yarda da ciwon da suke ji a zuciyarsu ba saboda haka basa neman hanyar ma da zasu magance shi, a haka har yayi musu illa wasu ma su shiga abinda ake kira da depression wanda kan kai ga kashe kawukansu.

2. Kayi bakin ciki na wani dan lokaci. A hakikanin gaskiya babu laifi idan kayi bakinciki akan abinda ya faru a kanka. Ina yawan bawa mutane shawar cewa idan abu bazai kai shekaru goma yana damunka ba, to kar ka bata mintuna goma ka alhini akansa.

Misali anan shine, idan tace bata sanka kaima kasani cewa bayan shekaru goma tabbas ka manta da rayuwarta ma, to don haka mai zaisa ka damu kanka na mintuna goma akanta. Wannan abun da nake fada yana da matukar wahala sosai, amma kamar yadda na fada idan alhinin da zakayi na wani dan lokaci ne kadan, to wannan babu matsala a tattare dashi.

Idan kana neman taimako yadda zakayi alhinin, zaka iya samun waje ka zauna kai kadai kayi tiananin duniya, ko kuma ka dinga tafiya kai kadai ba tare da kana hira da wani ba kamar na mintuna goma zuwa sha biyar.

3. A bada tazara. Idan ka kasance kana tare da wanda kake so amma baya sanka, yana da kyau ka dan bada tazara domin ka rage yawan haduwar da kukeyi. Bawai ina nufin mutum ya zama mugu ba ko kuma yaji cewa yaki jinin wanda baya sanshi bane. Sannan kuma bana nufin ka daina kula mutumin gaba daya, ko kuma ka yanke duk wata alaka dake tsakaninku.

Abinda nake nufi shine idan kuna saba haduwa a hanyar tafiya, to sai ka daina bin hanyar sai bayan sati sati. Ko kuma idan an saba zaunawa ne ana hira, to sai a rage yawan hirar da akeyi. Idan kuma wajen aikinku daya, to sai a ding gaisawa kawai bawai sai an dinga dariya ana lanbarai ba, domin hakan yana saka soyayya.

Sannan kuma idan kun saba magana ta yanar gizo to yana da kyau ku daina domin bai zama dole ba, ko kuma da katange mutum domin ka daina ganin abubuwan da yakeyi a yanar gizon. Idan da hali kuma, zaa iya goge lambar wayar mutumin domin kar tsohuwar soyayya ta jawo a tura sako ko kuma ayi kira ma.
4. Kar ka dinga karyata so. Idan mutum yace baya sanka ko kuma aka fada maka cewa bazai iya sanka ba, ba daidai bane ka dinga cewa ai dama nima ba sansa nake ba. Wannan zancen kasan karya kake wa kanka. Bahaushe ai yayi gaskiya daya ce ‘ance da makaho da ido yace baya so domin idon wari yake’. saboda haka shwara ta anan itace mutum ya yarda cewa akwai wannan son a zuciyarsa domin ya nema masa magani.

5. Ka guji fara shaye-shaye, kiranta a waya ko kuma tura sakon rubutu. A farkon yanayin da mutum ya gane baa san shi, yakan shiga damuwa sosai wanda wasu kan fara shaye shaye. Yin hakan bazai bada masalaha ba. Bayan nan kuma wasu suna ci gaa da kira a waya ko kuma su tura sakonni na rubuwa, shima yin hakan kunci kawai zai karawa mutum. Ka goge lambar

6. Baka da iko akan so. Karin bayani akan abinda nayi bayan a baya shine ka yarda cewa baka da ikon akan dole sai wanda kake so ya soka, ko kuma kai ka daina sonsa lokaci daya. Yawncin mutane zakaji suna cewa ‘ai dole ne ta fara sona’ da sauran irin wadannan maganganun da ba gaskiya bane. Ita soyayya da kuke gani ana gina tane akan halaye na yau da gobe ba wai dare daya ba. Saboda haka, ka gane cewa ba laifinka bane don baa sanka ba, kuma ba laifinka bane domin kana soyayya.

7. Kar a ajiye kyaututtuka. Idan kasan akwai abinda zai dinga sawa kana tinawa da soyayyar, to yana da kyau da rabu da wannan abun. Misali idan ta taba yi maka kyau wani abu, to idan abun nan yana nan sai ka bayar dashi ga wani. Idan kuma ba abinda zaka iya kyautarwa bane kamar zaman da kukayi tare a wani wani lokaci, to duk lokacin daka tina da wannan sai ka dinga kokarin dauke hankalinka da wani abun.

8. Ka kashe lokacinka idan baka yin komai. Zama waje daya mutum baya komai yana kawo tinani kala-kala musamman idan mutum yana cikin wannan yanayin na rabuwa da wanda yake so. Domin kashe lokacinka, zaka iya kiran abokinka kuyi hira ko ka kalli TV, jin radio ko kuma karanta littafi.

9. Ka nuna damuwarka. Akwai hanyoyi daban daban da mutum zai iya nuna damuwarsa kdan daga ciki sun hada da:
- fadawa wa wani damuwar
- Fada wa kanka da kanka damuwar
- Zubar da hawaye
- Karanta kurani

Sanna yana da kyau mu lura da cewa idan zamu nuna damuwar mu bai kamata mu dinga ihu ko kara ba, ko kuma mutum ya dinga bugun abubuwa da fasa abubuwa. 

Masana sun gano cewa yin hakan yana kara fushi ne ma a karshe. Amma idan ta kana mutum ya zubar da hawaye ai ba wata matsala bace domin masana sun gano cewa hakan yana taimakawa jikin mutum.10. Kayi lissafin abubuwan da kake dasu na gwaninta. Yawancin mutune idan idan aka nuna baa sansu, sai su fara tinanin ai basu da wani abu na baginta ko gwaninta. Saboda haka idan haka ta faru a gareka sai ka dinga tinawa kanka abubuwan da kake dasu na kirki da baginta wadanda wanda baya sanka yayi asarar su ta hanya kinka. Idan ka kasa tina abbubuwan da kake dasu na bajinta, zaka iya neman taimakon abokinka domin ya zayyano maka su.

11. A guji yin zargi. Kamar yadda na mabata a baya cewa mutum bashi da ikon akan soyayyarsa da ma soyayyar wanda yake so. Saboda haka, idan aka nuna baa sanka, kar ka dinga zargin wanda yace baya sana naka, ka dinga magnganun batanci akansa, ko kuma ka dinga zargin meyasa bazai fara sanka ba shima. Idan kayi haka baka yi masa adalci ba. A lura da cewa abokanai ko kawaye zasu iya zuga mutum cewa ai laifin dayan ne da baya sanshi, idan hakan ya faru abu mafi kyau shine kayiwa abokanan naka godiya amma ka fahimtar dasu cewa bai kamata su dinga batanci akan wanda baya sanka ba, yana da kayau ayi mata/mishi uzuri akan abinda bashi da iko akai.

12. Ka karfafa alakarka da sauran mutane. Yawancin mutane idan aka nuna baa sansu, sai kaga sun yanke alaka da kusan koa. Wannan ba dai-dai bane, abinda ma ya kamata kayi anan shine ka karfafa alakarka da sauran mutane domin koda basu ike maka gurbin ba zasu taimaka sosai. Zama da mutane masu fara’a da raha zai taimaka.

13. Ka gane cewa mutumin daya ki ka shima yana shiga cikin damuwa. Daga binciken da masana sukayi sun gano cewa duk lokacin da kake nuna soyayya sannanaka nuna cewa baa sanka, to ba kai kadai ne kakae shiga cikin damuwa da kunci ba, shi kansa wanda baya san naka yana shiga wani yanayin damuwa .

14. Ka fadawa wani matsalar. Yawanci idan mutum yana cikin fushi ko bakin ciki sannan kuma ya rike shi a ransa bai fadawa kowa a, to abin yafi cinsa a rai. Saboda haka, yana da kyau ka fadawa koda abokinka ne matsalar da kake ciki, koda kuwa baka tinanin zai taimaka maka da komai. Amma ka tabbatar ka yarda da wanda zaka fadawa damuwarka domin ba kowa ne yake son cigabanka ba.

Kar ka dinga tsammanin cewa kowa zai fahimci matsalar da kake ciki, saboda haka idan kasan akwai wanda ya taba shiga cikin irin wannan matsalar kuma ka yarda dashi to shi yafi cancanta ka fadawa.

15. Ka daukeshi a matsayin darasi. Hausawa suna cewa abinda babba ya hango, yaro ko ya hau dutse bazai iya gano shi ba. Wannan zancen nasu gaskiya ne domin shi mutum mai yawan shekaru ya hadu da darusa kala-kala sama da mai karancin shekaru. Daya daga cikin darusan zai iya kasancewa wani yace baya sansu. Saboda haka, ka dauki wannan a matsayin darasi a rayuwarka da zaka bawa wasu shwara nan gba akansa.

16. Ka gane lokacin ci gaba da rayuwa. Idan mutum ya shiga irin wannan yanayin na kin soyayya zai ga duk ya daina san wasu abubuwa. Saboda haka ka gane lokacin daya kamata ka cigaba da rayuwarka ta da. Misali idan kaga alamar abubuwan da mutane sukeyi ya fara baka sha’awa to alama ce ta cewa lokaci yayi da zaka manta da soyayyar ka cigaba da rayuwa.
A LURA
Saboda haka idan kana so ka daina san wanda baya sanka sai ka lura da wandannan abubuwan:
- Kar ka zari kanka.
- Kayi bakin ciki na wani dan lokaci.
- A bada tazara.
- Kar ka dinga karyata so.
- Ka guji fara shaye-shaye, kiranta a waya ko kuma tura sakon rubutu.
- Baka da iko akan so.
- Kar a ajiye kyaututtuka.
- Ka kashe lokacinka idan baka yin komai.
- Ka nuna damuwarka.
- Kayi lissafin abubuwan da kake dasu na gwaninta.
- A guji yin zargi.
- Ka karfafa alakarka da sauran mutane.
- Ka gane cewa mutumin daya ki ka shima yana shiga cikin damuwa.
- Ka fadawa wani matsalar.
- Ka daukeshi a matsayin darasi.
- Ka gane lokacin ci gaba da rayuwa.

No comments:

Post a Comment