Saturday, 12 January 2019

Yadda Ake Cire Tsami (Acid) Daga Tumatir


Hanyar farko: amfani da baking powder

A Yanka tumatir zuwa ƙanana: ya danganta da irin girkin da ake yi, saboda haka za’a yanka tumatirin dai dai da yadda ake buƙatar sa acikin abincin. A kula da cewa ƙananan yanka sunfi yin ɗumi da wuri.

A ɗora akan wuta zuwa mintuna 10: idan za’a zuba tumatirin ne a cikin wani abincin mai zafi, to ba sai an barshi akan wuta sosai ba. Amma a lura cewa idan kar wuta tayi yawa sannan kuma idan anyi yanka manya to sai an barshi zuwa lokaci mai ɗan tsayi. A tabatar cewa bai narke ba ko kuma ya ƙone.

A sauke sannan a zuba baking powder: za’a zuba kwatan  cokalin shayi ne a cikin tumatirin ne. Wannan yana aiki ne idan akayi amfani da kamar tumatir matsakaita guda 6. saboda haka sai a kwatanta idan tumatiran sunfi haka yawa ko basu kai haka ba. A lura da cewa za’a ji wani sauti idan aka zuba baking powder din.

A zuba sauran kayan girkin: bayan ya gama wannan sautin za’a iya suba sauran kayan girkin domin ci gaba da girki.
Hanya ta biyu: cire ‘ya’yan tumatirin

A cire ‘ya’yan tumatir ɗin: a yanka tumatir biyu a tsaye sannan ayi amfani da cokali ko wani abun wajen cire ‘ya’yan cikin tumatirin. Yawancin tsami/acid na tumatir yana cikin ‘ya’yan ne. Amma a lura da cewa akwai girkin da yake buƙatar ‘ya’yan tumatir ɗin.

A rage lokacin girka tumatir din: tumatir yana kara yin acid idan ya dauki lokaci mai yawa akan wuta, saboda haka  rage lokacin girka shi yadda za’a iya. Yana da kyau ace ba’a girka tumatir sama da awa daya da rabi ba.

A saka tumatir ɗin a ƙarshe:idan tumatir baya cikin manyan kayan girkin da ake yi ba, za’a iya zuba shi a ƙarshe bayan komai ya kusan gama dahuwa. Misali idan girkin awa daya ne to za’a iya zuba tumatir din a mintuma goman ƙarshe.

Yin amfani da tumatir da ba’a dafa ba: kamar yadda na ambata a baya, dafa tumatir yan jawowa acid ɗin ciki ya ƙaru. Saboda haka idan za’a iya amfani da tumatirin a haka to yana da ƙyau ayi.

Hanya ta uku: zaɓen tumatir mai kyau:

Ayi amfani da tumatir daya nuna: tsami/acid na cikin tumatir yana raguwa idan tumatir yana nuna. Saboda haka sai a zaɓi tumatir daya nuna sosai. Za’a iya gane wanda ya nuna ta hanyar jinjina nauyin sa da kuma matsa shi kadan, sai a zaɓi wanda yake da nauyi da kuma laushi kaɗan.

A girka su da sabon tumatir: idan aka siyo tumatir na leda ko na gwangwani za’a iya rage tsamin sa ta hanyar soya shi tare da sabon tumatir.

Yin amfani da wanda baiyi ja ba: tumatir yana zuwa a kaloli kamar ja, yalow, orange, kore da kuma haɗe-haɗen waɗannan kalolin. Masana sunce tumatir da baiyi ja sosai ba bashi da tsami sosai kamar wanda yayi ja sosai.No comments:

Post a Comment