Saturday, 5 January 2019

Yadda Zamu Kare Al-Adunmu Daga Lalacewa
Al’ada ita ace ginshikin al’umma, duk al’ummar data rasa al’adunta haqiqa ta dauko hanyar lalacewa.

Sanin kanmu ne cewa akwai al’adu da dama da suka ‘bata ‘bat a doron qasa sabo da rashin adana al’adunsu da suka gada tin iyaye da kakanni.

Anan zamu ga abubuwan da zamuyi domin ajiye abubuwan al’adunmu, ta yanda bazamu ji kunya ba yayin da ake so asan asalinmu.

1. Ya zama dole matasa su maida shigarsu, da kuma abin cinsu kai harda ma na shan su ya zama na gargajiyanci.

2. Ya zama wajibi matasa da yara su dinga zama da tsofaffi domin su koya musu al’adunsu da aka daina yi a baya domin su habbakasu.

3. Ya kamata a dinga koyawa yara yarikansu a makarantun su, in zai yiwu ma a dinga koyar dasu da yaren nasu, domin cin gaban al’adu.

4. Dole al’umma tasan yaya mutanan farko sukayi addinansu, domin sanin cikakkiyar yadda al’adar tasu ta samo asali.

5. Ya kamata duk wani biki da ake yin sa na al’ada, shin bikin nan shekara-shekara ne ko kuma wata-wata a ci gaba da yin sa kar a fasa.

6. Dole matasa su rage yawan yin wani yaren idan ba nasu ba, indai a junan su ne, su yawaita yin wannan yaren.
7. Ya kamata matasa su nemo hanyar adana al’adun su, misali: ta hanyar ajiye su a yanar gizo-gizo da makamanta hanyoyi ajje ababan tarihin.

8. Yawaita auratayya tsakanin qabilu daya, kan tabbatar da wanzuwar yare a doron qasa.

9. Duk abubuwan da muka sani mutanan farko sun qirqiro shi da basirar su, to ya zama dole mu ajiya shi a wuri me mahinmanci, saboda daukaka darajar al’adarmu.

10.  Mu dinga nuna al’adunmu a duniya, domin hakan kan saka duniya tasan damu, kuma darajar qabilarmu da al’adarmu ta qaru a idon al’umma.

No comments:

Post a Comment