Sunday, 20 January 2019

Yadda za ki/ka fara hira da budurwarka/saurayinki a haduwar farko

Samari da ‘yanmata da yawa suna shiga damuwa a loqacin da aka ce zasuyi hira da masoyinsu a karon faari. Wasu loqutan sai kaji ko wannensu yayi shiru saboda ba su san dame zasu fara maganar ba, a ko yaushe a wurin wadanda basu saba ba, qirqirar hira ba abu bane mai sauqi yana bawa mutane da yawa wahala wajan ta yanda zasuyi su fara. Anan zamu iya cewa kun zo inda za’a kwantar muku da hankali domin munyi wannan rubutune musamman saboda mu cire ku daga wannan tsoro da kuke ji duk loqacin da kuka hadu da masoyanku domin tattaunawa don fahimtar junansu.

Abin kunya sai kaga wani yaje wurin masoyiyar sa da niyyar yin awa uku sai kaga ko minti goma bai yi ba ya dawo, saboda rashin sanin makamar ta inda ya kamata ya fara zancen nasa. Ku saurara sannan ku bude kunnuwanku da kyau domin fahimta tare da haddace wadannan abubuwa da zamu fada don ku samu masoyanku su daina ginsar ku, ya zama cewa basa so ku tafi ku barsu, saboda dadin hirar da kuke yi tare da su.Kada ku ce zaku fara da doguwar hira, misali ku fara da gaisuwa sai kuma ‘yan qananun tambayoyi wadanda basa buqatar doguwar amsa. Sannan sai a tafi masu buqatar doguwar hira, misali, yau mai kika/ka yi? Da tambayoyi irin wadannan dai.

Kada kace/kice ke/kai kadai zaka/zaki rinqa Magana ko bada labara, idan ka/kin bashi/bata labara sai ki/ka tambayi ra’ayin sa/ta akan me ya/ta ke gani game da labarin.

Ku dinga yawan tattaunawa akan rayuwarku anan gaba, yaya zaku kula da ‘ya’yanku, yaya rayuwar auranku zata kasance.

Kada ku ce zaku boyewa junanku abubuwan rayuwarku, maimakon haka kuyi qoqari ku shigo da maganar cikin hirar ku domin ku tattauna akan ta.

Ko yaushe ku nuna wa tsarin rayuwarku, ku yi wa kanku Magana akan ra’ayin da kuka sha banban domin ku samu ku daidaita su loqacin da kuke hira mai tsayi.

Abu mafi muhimmanci, kada ka/k ice zaki/ka raba hankali yayin fara hirar, misali, ka/ki na son a fara hirar kuma ki/ka na danna waya, ko kallon film, ko cin abinci. A ah ka bata/ ki bashi hankalinki/ka gaba daya tare da kallon ta/shi yayin fara maganar 

No comments:

Post a Comment