Tuesday, 8 January 2019

Yadda zaku daina yin abinda kuka shaku dashi kuma kuna son ku daina (Addiction)


Mutane da dama suna da wasu abubuwan da sun saba dasu sosai, walau abin mai kyau ne ko mara kyau, kuma zasu iya sadaukar da komi nasu domin su daina aikata wannan abin. Abinda ake kira da addiction a turance. Ba lalle abin nan ya kasance mummunan abu ba, amma a loqacin da ya zamana cewa kana so ka cire shi daga rayuwarka to ya koma mummuna. Misali akwai mutane da dama da suka saba da shan leman nan da kowa ya san shi da koka kola, har takai ga in kullun basu sha ba basa jin dadi, wasu mutanan zamu ga su kuma goro ne nasu, wasu giya, wasu kuma tabar sigari, abubuwa da dama dai, ya danganta da yanayin mutanan da kuma abinda suka saba dashi. Anan zamu duba matakan da masu irin wannan halin zasu bi domin su rage har sukai matakin da zasu daina.

1. Abin farko daya kamata masu irin wannan halin suyi shine, su tinani kaana su zauna su lissafo abubuwan da suke saka su irin wannan halin, su duba suka in sun daina wanne irin canji zai kawo ga rayuwarsu da lafiyarsu baki daya.


2. Sannan sai suyi qoqari su kawar da duk wani abu yake tina musu da wannan abin, misali idan giya ce, suyi qoqari su kawar da duk kwalaban giyar gidansu, kuma su daina bi ta hanyar da ake siyar da ita.

3. Sai su duba a wanne loqaci suka fiya yawan sha ko yin wannan abu, sai su qirqiro wani abu mai amfani a madadin wannan su dinga yi a wannan loqaci. Misali; gudu, girki, ziyara, karatun littafi, motsa jiki da sauransu.

4. Su nemi shawarar makusantansu akan me suke ganin zasuyi domin su daina wannan abin da suke.

5. Yayin da ka/kika ga ka/kin fara ragewa sosai,se ka/ki sami wata rana muhimmiya, a matsayin ranar da zaka/ki daina wannan abu. Misali; ka saka nan da shekara 2 zuwa 3.
No comments:

Post a Comment