Monday, 7 January 2019

Yadda Yan Mata Suke Son Samarinsu Su Kasance.

   

Yana daga cikin abinda kowa ya sani cewa, samari da dama in sun zauna basu da hirar data wuce ta ‘yan mata, haka zalika suma ‘yan matan hirar tasu dai baata wuce ta samarin. A mafiya yawancin loquta ‘yan matan suna fadin irin kalar samarin da suke da sha’awar su samu a matsayin mazajen aure. Mun san maza da yawa zasu so suji irin wannan tattaunawa da ‘yan matan sukeyi a junansu. Sanin kanmu ne cewa mafiya yawancin samari basu da burin da ya wuce su burge ‘yan matansu. To ba sai ka wahalar da kanka ba wajen tambayar kowa game da haka, anan zakuji irin kalar saurayin da ‘yan mata suke burin su samu, ko yadda suke so saurayi ya kasance kafin ya burgesu.

1. ‘yan mata suna son saurayi ya kasance ba qazami ba, wato koda ace kayansa kala biyu ne kacal, suna so suga ko yaushe tsaf-tsaf yake ba maganar qazanta a tattare dashi.2. Mata suna so su sami saurayin da zai kasance abokinsu kuma masoyinsu, ma’ana, ya zama cewa yana sakar mata fuska sosai, ta yadda duk wani abinda zata gayawa qawarta to shima zata iya fada masa. A taqaice kar ya zama kamar wani boss, kullun a cukule, kamar wanda aka aiko masa da saqon mutuwa.

3. ‘yan mata da yawa suna son saurayi ya dinga tarairayar su kamar yanda zai wa yarinya, hakan ba yana nuna cewa idan anzo maganar da take buqatar nutsuwa ba, aqi nutsuwar.

4. Budurwa tana buqatar saurayi me tausayi da jin qai a gareta, tana so idan abu ya same ta na kuka, ya tayata kukan, idan na farin ciki ne, ya taya ta farin cikin.

5. ‘yan mata da dama suna so samarinsu su rinqa nuna su a ko ina, ma’ana basa jin kunyar nuna wa jama’a cewa wannan budurwata ce. Hakan yana sa farin ciki a cikin zuqatansu da matuqar jin dadi.

6. Duk wanda yasan mata a yanzu, yasan cewa idan zasu kalle ka daga qasa suke fara kallonka, takalmin ka suke fara kalla, kafin ragowar kayan jikinka, a taqaice mata suna son suga saurayi yasa takalmi mai kyau, musamman in yana da dama ya qara da agogo.

7. Mafiya yawancin mata ba su fiya damuwa da yanda kake da qarfin jiki ba, basa damuwa da yadda ka murmure de kwanjin ka, matuqar baka musu abinda suke so, ba abinda murdewar ka zata amfana maka a nan bangaran.

8. Sannan mata suna buqatar saurayin da zai girmama su, ya basu girman da su kansu sun san basu kai wannan matsayin ba, in ta yi kwalliya kada yayi shiru, ya nuna mata duk duniya ba wacce ta kai ta kyau da iya kwalliya a wurinsa. Ka riqe wannan sosai, suna matuqar son ziga ba kadan ba.

9. ‘yan mata da yawa suna son saurayin zai dinga yawan kiransu a waya, saqon karta-kwana ba kama qafar yaro, ko yaushe hankalinka na wurinta.


10. Abu na qarshe mace na son saurayi mai yawan barkwanci, duk halin data shiga na qunci da bacin rai, yana zuwa zai saka ta manta da duk wadannan matsalolin nata.

1 comment:

  1. Yan mata dayawa Suna son saurayin da zai dinga kiransu a waya.

    to idan batada wayafa Dan naji malamai Suna cewa bai kamata budurwa ta rike waya ba.

    ReplyDelete