Tuesday, 15 January 2019

Yadda ake wankan janaba

               
                
Wankan janaba ya kasu gida biyu a musulunci, akwai irtimasi da kuma tartibi. Malamai sunyi bayani akan ko wanne, kamar yadda zamu dauke su daya bayan daya muyi bayanin yadda ake yin su.

TARTIBI

Wannan wanka ne da ake yinsa daki daki, wato daga wannan sai wannan. Ga yadda ake yinsa:


1. Niyya. Sanin kowa ne cewa dukkan aiyuka basa tabbatuwa sai da niyya.

2. Sai yayi bismillah, sannan ya wanke hannuwansa sau biyu (2) ko sau uku (3) kafin ya tsoma su a cikin mazubin ruwan. Sannan ya wanke al’aurarsa, domin kawar da duk najasar da take jiki.

3. Daga nan kuma sai mutun ya wanke hannuwansa da sabulu ko toka ko kuma qasa. Sannan ya tsoma hannunsa a cikin ruwan domin yin alwala, kamar yadda yake alwalar salla amma bazai wanke qafafunsa ba indai akan turbaya yake wankan, wasu malaman suka ce in akan siminti ne ko abinda yayi kama da haka za'a iya wanke qafafu.

4. Sai mutun ya ɗebo ruwan a hannunsa ya cuccuɗa kansa, saboda gashin kan nasa ya koma daga budewar da yayi sanadiyar fitowar maniyyi. Sai ya ciko tafin hannunsa da ruwa ya zuba a kansa, ya tabbatar  ruwan ya ratsa ko ina a kan nasa, yayi haka har sau uku (3).

5. Daga nan sai ya ɗebi ruwan ya kwara a gefen jikin sa na dama, ya tabbatar ruwan ya taɓa ko ina, sai yayi hakan a ɓangaran hagunsa. Ya kamata mutun ya kula da irin ƙasan gwiwar sa da matse matsin sa, ya tabbatar ruwan ya shiga wadannan wurare.

IRTIMASI

Shi wannan wankan ya banbanta da tartibi.  Ana yinsa a wurin da ruwa yake mai yawa. Wanda zai yi wannan wanka zaiyi bismillah, sannan ya wanke hannayensa ne sau 3, sai ya wanke al'aurarsa domin gusar da najasar data sameshi, daga nan zai fada cikin wannan ruwa domin wanke jikinsa baki daya.


Duka wadannan wankan janabar, ya halatta ayi sallah dasu. Kamar yanda yazo a hadisai da dama.

Allah yasa mu dace.

1 comment: