Thursday, 17 January 2019

Yadda ake wankan gawa

                                  

An so duk wani musulmi yasan yadda ake wankan gawa, abinda zai bamu mamaki shine, musulmai da yawa wallahi basu san yadda ake wankan gawa ba. Kuma abin baqin cikin harda daliban ilimi a cikin wadanda basu iya dinba. 

Wanda zai yi wankan gawa an fi so ya zama mutun baligi, kuma mai amana, ba wanda zai je ya dinga surutu akan wani abu daya gani a jikin mamacin ba, ya kasance mai kame bakin sa akan wannan gawa da yayi wa wanka, sannan anso ace idan namiji ne ya mutu to maza su wanke shi, kamar yadda shari’a ta tanada, in mace ce ya zama mata, kuma anfi so makusantan mutun suyi ma gawarsa/ta wanka. A wankan gawa ana buqatar mutane uku (3) ko hudu (4) su wanke ta.

Ana wanke gawa sau uku ko hudu ko yanda masu wanke gawar suka ga yayi musu ( kamar yadda manzon Allah s.a.w ya fada wa masu wanke ‘yarsa) kawai dai ana so ya zama wutiri.

1. Za a kwantar da gawar, sannan a lullube tsiraicin ta, za a daga kan gawar domin ruwan da ake wanketa ya dinga gangarawa sosai.


2. Mai wankin zai fara da Bismillah, za’a wanke duk wata najasa da take jikin gawar wacce ta fita loqacin fitar ran mamacin. An so ayi amfani da sabulu da ruwa.


3. Za a dan danna cikin mamacin saboda abubuwan da basu gama futowa ba su fito, sanna a qara wankewa da ruwa.


4. Za a wanke inda aka rufe na daga tsuraicin gawar.


5. Za a yiwa mamacin alwala kamar yadda ake alwalar salla, amma ba tare da an saka masa ruwa a baki da kuma hancin sa ba. Za a yi amfani da dan qaramin tsumma ko auduga domin goge mai haqora da hancin nashi.


6. Idan mace ce za’a kunce gashin nata a wanke shi, a taje shi, sannan ayi mai qulli uku. Idan namiji ne kuma za a wanke gemun sa sosai.


7. Kada a manta ko yaushe, za a fara gabatar da bangaran dama sannan na hagu, kuma ko yaushe sai an fara wanke kai zuwa kafada, kafin kafadar zuwa qafa.


8. A wankin qarshe sai a saka kamfo, ko wani tiraran da ruwa.


9. wasu suna samun wani tsumman mai kyau domin tsane ruwan jikin mamacin.


10. Daga nan sai kuma a shirya gawar domin yi mata suttura.Allah yasa mu cika da Imani.

Amen 

No comments:

Post a Comment