Monday, 14 January 2019

Yadda ake rage tumbi cikin nishadi

     

Mutane daban daban suna da tumbi irin nasu, wasu zamu ga hutu ne ya kawo hakan, wasu kuma wahala ce ta ke kawo musu, wasu yawan shan giya, wasu kuma musamman a mata bayan sun haihu akwai tumbi da yake fito musu. To koma dai menene sila, anan zamuyi bayanin hanyoyin da za’a bi domin rage girman shi wannan tumbin.

TUMBIN WAHALA

Akwai wdanda zamu ga cewa tumbinsu ya samo asali ne saboda dadewar da suka yi suna aikin wahala, ba lalle aikin nan ya zama na qarfi ba, yawan aiki a ofis, yawan zirga zirga ba qaqqautawa, duka wadannan sukan iya jawo tumbin wahala. To abu mafi sauqi da mutum zai yi shine, ya samar wa kansa sauqi, ya rage yawan wadannan abubuwa da yake, domin in ba haka ba, yana yiwuwar haduwa da cutar sakari wato diabetes. Bacci isashshe shine yafi cancanta ga irin wadannan mutanan.
TUMBI BAYAN HAIHUWA.

Wasu matan bayan sun haihu suna yin dan tumbi, wanda da yawwansu basa son hakan. To hanya mafi sauqi da zaki rage wannan tumbin shine ta hanyar motsa jikin ki. Yawancin irin motsin da likitoci suke cewa ayi shine. ki kwanta a kan bayanki, ta yanda hannayenki ma zaki saka su ta bayan, sai kid an tankwashe qafafunki kadan ki dinga motsawa, kamar dai yanda masu iyo a ruwa suke yin iyon baya. Hakan itace hanya mafi sauqi da tumbin zai ragu.

TUMBIN SHAN GIYA

Ga ma’abota shan giya kuma, giya tana taimakawa matuqa wajan ajiye tumbi, domin giya tana hana kitsen dake jikin mutum ya narke. To matsawar kana so ka rage timbin ka wanda shan giya ne ya kawo shi, ya zama dole kayi wadannan abubuwa. Na daya dai ya kamata ka rage shan giyar, abu na biyu kuma dole ka riqa shan ruwa sosai, sannan ka dinga yawan cin kayan marmari da kuma ganyayyaki.

  TUMBIN JIN DADI.

Akwai wadanda zamuga cewa, yawan cin kayayyaki abinci da yawa kuma kala-kala yake kawo tumbin, wasu zamuga cewa da kyar suke ska wandonsu ko kuma ta saka siket dinta, saboda timbin yayi girma, wani ma zamuji an ce da tumbin sa yake tuqa motar sa. Na tabbatar mutun zai so yaji hanya mafi sauqi da zai rage wannan tumbi nasa. Ya yawaita motsa jikin sa domin haka hakan zai taimaka wajan qona man da ya taru a jikin, ya kula da abubuwan da yake ci, duk abinda yasan zai qara mai yawan kitse to ya yi wa kansa tsaiwar dare ya rage cinsa.
No comments:

Post a Comment