Saturday, 12 January 2019

Yadda ake hada hallaka kobo

   

Hallaka-kobo wani kayan kwalan da maqulashe ne na hausawa da suke yi, domin kwadayi. Ga yadda ake hada shi.


1. Da farko mai girki zata samu sikari  adadin yawan da take so ta hada, se kuma gyada da kuma man gyada.

2. Zaki zuba gyadar taki a tirmi, ki dan daddaka ta kadan, se ki cire ta, ki bushe, ta yanda wannan jan na jikin gyadar zai fita.

3. Sai ki mayar da ita tirmin, ki daka har sai ta zama gari, ma’ana tayi diddiga, kar ki bari tayi mai.

4. ki dauko kasko ko tukunyar ki, ki dora ta a kan wuta, sai ki zuba sikarin a ciki, kina jujjuyawa har sai ya fara canza kala. yana komawa kalar qasa qasa sai kiyi sauri ki zuba wannan gyadar cikin kaskon. Kada ki bari sikarin ya qone, in ya qone hallaka-kobon zai ‘daci.
5. Ki rinqa juya sikarin da gyadar har sai sun kama jikinsu. Ki samu faranti ki shafa masa man gyada, daga nan sai ki sauke hallaka kobon daga wuta, ki tsiyaye shi a cikin farantin da kika shafa ma mai.

6. Sai girgiza farantin ta inda hallaka kobon zai baje a cikin farantin, idan kuma yayi kauri, to sai ki nemo cokali ki baje shi, yana fara shan iska, sai kisa wuqa ki yayyanka shi. Daga nan sai ki jira ya bushe.

Ba abinda ya rage sai ci.

No comments:

Post a Comment