Tuesday, 8 January 2019

Yadda ake hada gwangwazo

   
Nasan mutane da dama basu san menene gwangwazo ba wanda wasu mutane ke kiransa da qundun kaza, musamman mutanan da ba a karkara suka tashi ba, wato mutanan birni.

Gwangwazo wani abinci ne da mutanan qauye ne suka fiya cinshi, abinci ne na gargajiyya, wanda inda wani zai ga ka/ki na ci sai ya dauka ko ba dadi ko kuma biki/baka san dadi ba. Amma batu na gaskiya in ka/kika tambayi ma’abota ci zasu baki/ka labarin yanda dandanon sa yake yayin da ka/kika saka shi a cikin bakinki/bakinka. Abinci ne mai qara lafiya bayan dadin da yake dashi a bakin mai cin sa.

Yanda ake hada shinkafa da wake kusan haka ake hada gwangwazo. Sai dai shi ba shinkafa da wake bane duk da shima ya kunshi waken a cikinsa, abinci ne wanda yake saka saurin qoshi a wurin wasu, idan kika/ka ci da yawa sai ka/ki wuni kana shan ruwa baka nemi komai ba. Amma mu sani ba kowa ne kejin qoshi da wuri ba  yayin da yaci.

Yanda ake hada gwangwazo ba abu bane mai wahala. Ku bamu hankalinku domin sanin yadda ake hada shi wannan abinci mai suna gwangwazo.

1. Da farko dai  mai girki zata tanaji waken ta da kuma gero. Ta fara wanke waken, sannan ta zuba shi a tafasashshan ruwan da ta dora akan wuta, saboda mun san yadda wake yake da rashin saurin dahuwa.
2. Sannan ta dauko wannan geron nata ta sirfeshi, daga nan sai ta tankade geron domin cire dusar sa, yayin da ta kammala cire dusar, sai ta wanke shi, sannan ta jira waken yayi alamar dahuwa.

3. kada ta bari waken ya dahu ligib sosai, sai ta zuba geron a ciki, wasu suna zuba gishiri a ciki kafin ya dahu, wasu kuma basa yi, daga nan sai mai girki ta jira dahuwar su.

4. Ya kamata mai girki ta lura da kyau wajan yanayin ruwa da zata zuba, ta fara duba yawan abincin nata, saboda cika ruwa kan saka gwangwazon ya cabe kuma bazai yi dadi ba.

5. Shi dai wannan hadi na wake da gero da ake kira da gwangwazo, ana cin sa da mai, maggi, da kuma yaji, musamman mutun ya samu man shanu, kunnan sa har rawa zai dinga yi saboda dankaran dadi.

Ya kamata ko sau daya ka/ki gwada, nasan daga baya zaku gode mun.

No comments:

Post a Comment