Wednesday, 30 January 2019

Yadda ake hada gam (gum) daga fetur

Na tabbatar mutane zasu yi mamaki, ta yaya za'a hada gam daga fetir.  To wannan abu ba abu bane mai wahala, domin kazo wurin daya dace domin koyar yaddaake hada wannan gam da ya samo asali daga fetir. Shi dai wannan gam za'a iya yin duk waniabu daka sani anayi da gam, dadi da qari kuma hanyar hada shi ba abu bane mai wahala.  Wanda munsan yanzu in mutum yace zai sayi gam me kyau to tabbas zai kashe kudade masu yawa. Ta wannan hanyar kuwa muna tabbatar muku cewa ba wani kashe kudi masu yawa akuma zaka samu gam wanda asalinsa daga qasa ne, wato natural gum inji bature. Daga jin sunan kai kasan cewa zai yi kwari da qarko kai bal ma yafi gam din da kake/kike siya qarfi. A sauqaqe da kwanciyar hankali zaka hada wannan gam. Ga yadda ake hada shi:

1. Mutum zai samu fetir dinshi daidai yawan da yake so gam dinsa ya zama. 

2. Daga zai nemo abinda ake kira da biredin mahaukaciya.  Ga wadanda basu sanshi da wannan suna ba, biredin mahaukaciya shine wani fari abu da idan mutum ya suwo sabuwar talabijin, radio, firinji, ko wani sabon abu da turowa suke yi na lartanki zaku ganshi a ciki, an tottokare gefe, qasa da saman wannan abun dashi, fari ne tas kuma yana dan qqsa in ka shafa shi. 

3. Mutum zai zuba fetir dinshi cikin kwano. 

4. Sai ya dauko wannan biredin mahaukaciya ya guggutsurashi. 

5. Sai ya dinga daukar wannan biredin mahaukaciyar yana tsomashi cikin fetir din, zaiji yana wata 'yar qara yana narkewa a ciki fetir din kamar ana narka qarfe. 

6. Ya ci gaba da saka wa har sai ya yi kaurin yadda yake so, sannan sai ya ajje shi ya jira ya huce. Domin yin amfani da shi.No comments:

Post a Comment