Monday, 14 January 2019

Yadda ake adana kifi ba tare da an saka shi a firinji baAkwai hanyoyi da yawa  da ake adana kifi ba tare da ya lalace ba kuma ba tare da an saka shi cikin firinji ba. Zamu dan tsakuro kadan daga cikin wadannan hanyoyi domin muyi bayani da a kansu ta yadda mutane zasu amfana dasu, musamman yanda muke cikin halin rashin wuta a wannan qasa tamu Nigeria.

SHANYAWA

A da can kafin zuwan firinji, masunta suna shanya kifi domin gudun lalacewarsa. Ba wai suna shanyar bane yadda suka ga dama kamar kaan wanki, a ah akwai hanyar da suke bi wajan shanyar. Da farko suna farka cikin kifin, ya danganta da masuncin, wasu suna rabashi gida biyu, wasu kuma suna budeshi amma ba duka ba, daga nan da yawansu suna samun asa bari su shimfida a qasa ko kan siminti in da dai rana zata dake shi, sai su baza kifin akai. Idan bai bushe a ranar ba, da daddare suna mai dashi cikin daki saboda gudun raba, sai washegari su qara fito dshi cikin ranar har ya bushe. In har ya bushe gaba daya to bazai taba lalacewa ba ko shekara nawa zaiyi, saboda gaba daya ruwan jikin say a qone balle har halittun da ka iya sawa ya lalace su fito.
ZUBA MASA GISHIRI.

Idan mutun yana inda yake yanayin wurin da zafi, yana iya samun kifinsa ya yanka shi gida biyu, daga nan sai ya debo gishirinsa ya barbada a cikin kifin da kuma kan fatar kifi, sai a saka kifin a kwano ko wani abu da dai zai dauke shi, a lullubeshi da tufafin da aka jiqa shi ba sosai ba. Wannan hanyar adana kifi ne na awa ashirin da shidu wato rana daya kenan.

No comments:

Post a Comment