Tuesday, 22 January 2019

Yadda Ranar Juma-ah Take Da Falala

Allah madaukakin sarki yana cewa cikin suratul jumu’a:” Yaku wadanda suka yi imani,idan anyi kira zuwa ga salla daga ranar jumu’a, sai kuyi aiki zuwa ga ambaton Allah, kuma ku bar ciniki, wancan dinku ne yafi alheri a gareku, idan kun kasance kuna sani”. (q.62,9)

Hausawa suka ce jumu’a babbar rana. Hausawa sunyi gaskiya, domin jumu’a tana da falala sama da ragowar kwanaki. A yau matasa da dama basu damu da zuwa sallar jumu a da wuri ba, yawanci an fi ganewa idan liman yana gaf da zai tada sallah sai a je cikin gaggawa. Wanda hakan ba daidai bane, a cikin falalar jumu’ar da zamu kawo anan gaba, zamuji darajar da wanda yaje masallaci sallar jumu’a karon farko yake dashi da kuma muhimmanci da amfanin jin khuduba.

 Mun sani cewa saboda daraja da girman wannan rana ya saka Allah s.w.a ya saukar da sura guda mai suna suratul jumua. Saboda a nuna mana cewa tana da falala fiya da wadancan ragowar ranaku.

Daga cikin falalar ta manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yana fada cikin hadisi cewa: “ Duk mutumin da ya mutu a dare ko yinin jumu’a Allah zai kare shi daga azabar kabari”. Tirmizi da Ahmad ne suka ruwaito.

Ahmad R.A  yace; manzon Allah s.a.w yace: “Duk bawan da yayi cikakken wanka sannan ya je sallar jumu’a da wurwuri, sannan ya tsaya yaji khudubar liman, kuma baiyi wani abu na wanda ba daidai ba, Allah zai bawa wannan bawan ladan azumi da sallar shekara guda”. Au kama qalal rasool s.a.w.

Sannan an karbo daga muslim r.a cewa, manzon Allah s.a.w yace: idan ranar jumu’a tazo, mala’iku suna tsayawa a ko wacce qofa ta masallaci, wadanda suke rubuta sunayan wadanda suka zo da farko, sai wadanda suka zo bayansu. Idan liman yazo ya zauna, zasu rufe abinda suke rubutun, sai suzo su zauna suji tinasarwa. Wato hudubah.” 

 Na tabbata Ba wanda bazai so ya shiga cikin sunayan da mala’iku suke rubutuwa ba, to mai zai hana ya kai dan’uwa ka dinga fita da wuri kafin fara huduba, ko a karon farin ma domin samun wannan gwagwgwaban lada.
Hadisi na qarshe da zamu duba wanda manzon tsira, annabin rahama s.a.w ya fada shine. “Ranar da tafi ko wacce rana wacce rana ke futowa cikin ta itace jumu’a. itace ranar da aka halicci Adam. Itace ranar da Adam ya shiga aljannah kuma ranar aka fitar dashi. Itace ranar da za’a tashi alqiyama”. Abu dawud, nisa’I, tirmizi da kuma muslim duk sun ruwaito wannan hadisi.

Wannan hadisin ya qara fito mana da falalar jumu’a qarara. Da fadin manzon Allah s.a.w cewa ranar aka halicci annabi Adam, wanda kowa yasan shine farkon halitta, kuma baban mutane baki daya, wannan ba qaramar falala bace da jumu’a ta kebanta da shi. Da fadin sa cewa ranar ya shiga aljannah kuma ranar aka fitar dashi, zamu san cewa ranar annabi Adamu aka sakko dashi izuwa duniya wadda a cikin ta yanzu muke. Sannan abu na qarshe fadin sa cewa ranar za ai tashin alqiyama, wannan itama falala ce babba, ace ranar aka sauko da babanmu annabi Adamu zuwa qasa kuma a wannan ranar dai za a nade qasar baki daya. 

A qarshe ana so a yawaita salatin manzon Allah s.a.w ranar jumu’a.

Allah yasa mu dace. Ameeen.


1 comment: