Thursday, 24 January 2019

Amfanin shinkafa a jikin dan adam
Mutane zasu iya mamaki cewa, daman shinkafa tana da amfani a jikin dan adam bayan maganin yunwa da take mai? Amsarku itace: kwarai ma kuwa, domin amfaninta ya wuce yadda mai karatu yake tsammani, domin ba iya qara lafiya ba har maganin wasu cututtukan take yi. Bara muji kadan daga cikin amfanin ta.

1. Shinkafar da ake kira “brown rice” a turance tana taimaka wa matuqa wajan daidaita yawan sikarin dake cikin mutum, hakan zai saka mutum ya cire tsammnin kamuwa da cutar ciwon sikari.

2. Qari akan haka kuma, shinkafa tana taimakawa garkuwar jikin dan adam, tana qarfafar ta domin yaqi da cututtukan dake shigowa jikin nasa.
3. Ita dai shinkafar nan mai suna brown rice tana taimakawa sosai wajan rage wa mutum ciwon gabobi.

4. Shinkafa tana taimakawa wajan rage yiwuwar kamuwa da cutar ciwon daji da aka fi sani da cancer a turance.

5. Shinkafa tana taimakawa wajan rage  yiyuwar kamuwa da cutar ciwon zuciya. Musamman ga mutanan da suke cin wannan da aka fi sani da brown rice din nan dai.

6. Babban aikin da shinkafa take shine ta bawa duk wani mai cinta qarfi, mutum yaji ya samu qarfin yin aiki.

No comments:

Post a Comment