Saturday, 5 January 2019

Yadda Ganyen Shayi Yake Da Amfani a Jikin Dan Adam

   
 

Mutane da yawa suna da sha’awar shan shayi a ko yaushe musamman da daddare, wasu ma sun maida abin kamar al’ada, ya zame musu in har basu sha ganyen shayi ba basa jin dadi.

Zamu so musan amfanin wannan ganyen shayin a jikin mu, shin da cutarwar sa da kuma amfaninsa wanne ne yafi yawa.

1. Idan ka/ki na jin ka/kin gaji da shan ruwa ko yaushe, to ganyen shayi yafi cancanta daka/ki nema, domin yana sawa ka/ki ji ka/ki na so ka/ki sha ruwa.

2. Ko kunsan cewa shan ganyen shayi kullun da safe yana kare ka daga ciwon zuciya.

3. Shin ka/ki na so ka/ki rage qiba? To ka/ki yawaita shan ganyen shayi, domin yana temakawa wajen qona man dake jikin ka/ki kuma ya qara ma kuzari.

3. Haqiqa na tabbata cewa ganyen shayi yana maganin ciwon gabobi, abinda bature yake kira da rheumatoid arthritis.

4. In ka/ki na tantama to yanzu kun tabbatar, domin ganyen shayi yana kare ka/ki daga ciwon sikari. Ku bincika na tabbatar likita zai tabbatar muku da haka.

5. Ganyen shayi yana temakawa wajen rage tashin hankali(stress), shi yasa mutane da yawa suke sha in sun tashi daga aiki ko kuma da daddare.
6. Shin kana yawan yin mura? To ba sai ka dinga yawan shan magunguna ba, da zarar ka samu ganyen shayin ka, ka tsoma shi cikin ruwan zafi, musamman ka hada shi tafarnuwa da citta, na tabbatar sai ka gode min.

7. Ko kun san cewa shan ganyen shayi yana qara kaifin basira, likitoci sun tabbatar da amfaninshi a kwakwalwa, ka yawaita sha kaga abin mamaki.

8. A cikin ganyen shayi akwai wani sinadari da ake kira da “flavonoid” da wadansu sinadarai da suke kare mutun daga samun cutar hawan jini.

9. Ganyen shayi yana maganin ciwon hanta da qoda, idan kana buqatar qarin bayani, nemi likitanka domin ya doraka akan hanya.

 10. Daga cikin amfanin ganyen shayi yana kare mutun daga kamuwa da cutar daji, wanda aka fi sani da suna “cancer”.

No comments:

Post a Comment