Saturday, 12 January 2019

Yadda Aya Take da Amfani a Jiikin Dan Adam

Aya kamar yadda bature ke kiranta da tiger nut, abinci ce da ake cinta yawanci dan marmari, wasu kuma suna ci yayin da suka ci suka qoshi domin jin dadin rayuwarsu. Anan zamu fadi amfanin ta a jikin dan adam, domin kuwa duk abinda ka gani a doron qasa yana da amfanin.

Aya da muka sani ana sarrafa ta ta hanyoyi daban daban, ana yin biredi me dauke da aya, cake me dauke da aya, kai har da abubuwan da baka tinani ana sarrafa aya domin ta qara wa wannan abin armashi. Ku saurara domin amfanuwa da wannan abinci da Allah ya bamu a araha, domin da naira goman ka ko ashirin za’a baka aya kaci har sai ka ture.

1. Aya tana da amfani sosai wajan qara qarfin qashi da kuma qara kyan jinni, indai kana yawan cinta, domin tana dauke da abinda ake da kira protein me yawan gaske a cikin ta.

2. Ko kunsan cewa aya tana maganin ciwon sigari, garzaya wajen likitanka da gaggawa domin ka tabbatar da maganata.

3. Iyayenmu da kakanninmu suna amfani da aya wajen warkar da matsalar cututtukan da suka shafi maza musamman matsalar saduwa da iyali.
4. Ana amfani da aya domin warkar da cututtukan da suka shafi ciki, irinsu gudawa, rudewar ciki da sauransu.

5. Game da mutanan da basa shan madara kuma, kunun aya yafi cancanta da su dinga yawan sha, domin zata basu nishadin da dadin da ake buqata a cikin waccan madarar kuma bazata cutar dasu ba.

6. Aya magani ce sosai domin kawar da cututtukan da suka shafi jinni, wanda suka hada da rashin gudun jinni yanda ya kamata. Kai ga masu yawan ciwon qirji ma, aya zata musu amfani matuqar gaske domin kawar da wannan ciwon nasu.

No comments:

Post a Comment