Monday, 17 December 2018

Yadda Zaki Gane Sati Nawa Kike Dauke Da Ciki


Sanin kwana nawa kike ɗauke da ciki abune mai sauƙi idan zaki iya tina ranar ƙarshe da kika ga al’adarki. Amma idan al’adarki bata da kyayyadajjen lokaci to kina buƙatar ganin likitan haske (Radiographer). yawancin mutane suna amfani da calculata ta yanar gizo-gizo domin gane hakan.

1. Yin amfani da calculatar ƙirga kwanankin ciki ta yanar gizo-gizo.
A nemo calculatar ƙirga ciki ta internet ta hanyar nama ta google. Ko kuma kiyi amfan da wannan: http://www.nhs.uk/conditions/pregnancy-and-baby/pages/due-date-calculator.aspx

A saka bayanai a ciki. Zaki saka bayanai da suka haɗa da ranar ƙarshe da kika ga al’adarki. 

Sai a tura musu bayanan. Da zarar kin gama amsa musu tambayoyin, sai ki tura musa domin su taimaka wajen gano miki kwanakin da kike ɗauke da ciki.

2. A je wajen likita domin a tabbatar cewa kina da ciki. 
- Abinda likita zaiyi na farko shine ya tabbatar cewa kina ɗauke da ciki. Likitan zaiyi miki wasu tambayoyi akan tarihi, al’adarki, maganin da kike sha da sauransu. Daga nan zai sa kiya gwaji a asibiti domin tabbatarwa.

- Likita zai dubaki. a wannan lokacin za’a gwada jininki, auna nauyinki. Domin ya faɗi cikin kwana nawa kike dashi, likita zai duba girman mahaifarki ta hanyar danna miki ciki. Ta wannan hanyar za’a fara kintatar kwanakinki nawa da ciki.

- Za’a tura ki wajen likitan haske: idan kikaje zaiyi miki abinda ake cewa ultrasound wanda zai nuna haƙiƙanin kwanakin cikin.


3. lissafa al’ada domin ganowa

- Likitoci da yawa suna gane satin da kike ɗauke da ciki ne bayan sunyi ƙirga daga al’adarki. Zai fara ƙirga ne daga ranar farko da kikaga al’darki ta ƙarshe.
Amma wannan lissafin yana aiki ne kawai idan kina da al’ada kyayyadajjiya. Misali duk bayan kwanaki ashirin da tara.
Wannan hanyar ba kowacce mace take wa aiki ba, sannan kuma lissafin zai fito daidai ne idan har kina ajiye tarihin ranakun da kike samun al’ada.
- Ƙirga makonni. Bayan kin gano ranar farko da kika ga al’adarki ta ƙarshe, sai ki ƙirga satin domin gano sati nawa kike ɗauke da cikin. Idan kina ƙirga makonnin kar ki fara da makon farko. Saidai idan kin gama satin farko, kenan kina da cikin sati guda. Saboda haka idan kina satinki na sha huɗu amma baki cika shi ba, kenan kina da cikin sati sha uku.

- A ƙirga lokacin tsammanin fitowar jaririn. Zaki iya tsammanin jaririnki bayan makonni arba’in da kike da ciki. Sai ki ƙirga makonni arba’in kenan gada daga ranar ƙarshe da kika ga al’adarki. Amma ki sani cewa babu tabbas a lokacin tsammani, jaririnki zai iya zuwa a lokacin daya so.

- A lura da cewa waɗannan kwankin basa nuna tabbas.

No comments:

Post a Comment