Thursday, 20 December 2018

Yadda Zakayi Idan Wayarka Ta Fada Ruwa

waya a ruwa

Faɗawar waya ciki ruwa bashi da dai ko kadan, sannan kuma zai iya jawowa wayar mutum ta daina aiki har abada idan ba'a san matakan daya kamata a ɗauka ba lokacin data faɗa cikin ruwan. Wayoyi suna yawan shiga ruwa ta hanyar wanki, wanka, banɗaki, miya, shayi ko ruwan sama. Shin wayarka ta faɗa ruwane ko kuma kana yin rigakafini ne saboda wata rana? Koma menene dalilinka, sai a biyomu a wannan rubutun.
1. A cire wayar daga cikin ruwan. Da zarar an ankara cewa wayar ta faɗa cikin ruwa ko abunda yake da ruwa, to sai ayi maza maza a ciro ta daga ciki. Idan baka cire ta da wuri ba ruwa zai iya shiga cikin wayar ta ƙofar chaji, earpiece da sauransu.

2. Kar a danna komai a jiki. Ina bada shawarar kar kayi ɗokin kunnan wayar saboda tabbatarwa tana aiki ko bata yi. Abinda yafi shine kar ka kunna ta, kar ka danna komai sannan kar kayi amfani da wayar ma gaba ɗaya.

3. A cire batiri. Idan wayar ana iya cire mata batiri to sai ka cire mata sannan idan tana chaji shima sai ka cire. Abin nufi anan shine ka cire wayar daga duk wata hanyar da zata bata wutar aiki.

4. A cire case/gida. Idan wayarka tana cikin gida ne, sai ka cire ta daga ciki. Kar ka dinga girgiza wayar domin gudun kar ruwan ya shiga wuraren da bai shiga ba ada.

5. A cire duk wani ɓangare mai ciruwa. Duk wani abu da zai ciru daga wayar sai ka cire shi. Misali layi, memori card da wasu abubuwan kamar earpiece, charger.

6. Ka tsane wayar da tawul ko tsumma. Ka sami tsumma ko tawul da yake a bushe kuma mai kyau sai ka tsane wayar dashi. Yin hakan zai tsane ruwan da yake wajen wayar ne kawai.

7. A guji bushe ruwan cikin wayar. Kar kayi ganɗokin bushe ruwan da yake cikin wayar. Hakan zai sa ruwan da yake ciki ya ƙara yin ɓarna ta hanyar shiga inda bai shiga ba ada. 

8. Kar a kwance wayar. Idan wayarka tazo da abinda ake cewa warranty, to bazan bada shawarar ka kwance wayar da kanka ba domin zai soke warranty din naka. Warranty shine kariyar da kamfanin wayar yake bawa wanda ya sayi wayr domin su gyara maka wayar kyauta idan ta lalace ko kuma su chanza maka wata. Amma idan baka buƙatar warranty ɗin sai ka kwance wayar taka domin ta bushe da kyau.
9. A busar da wayar. A baya nayi maganar a busar da ruwan da yake a waje da tawul. Anan kuma ruwan da yake ciki shima yana buƙatar ka busar dashi. Saboda haka zaka iya amfani da abun da ake kira da vacuum domin zuƙe ruwan ciki, ko ka saka ta a cikin shinkafa ɗanya, ko kuma ka saka ta a cikin abunda yake zuwa a cikin kwalin takalmi wanda ake kira da silica gel. Amma idan ka riga ka siyo gidan busar da waya tun kafin ta shiga ruwan, sai ka ɗauko shi domin ka sakata a ciki. 

10. A jira kwana ɗaya zuwa biyu. Ka jira har ruwan da yake cikin wayar ya tsane a cikin kwana ɗaya zuwa biyu. Idan kana da wata wayar sai ka saka layinka domin ka cigaba da amsa kira.

11. Ka duba ko wayar ta bushe. Bayan lokacin dana ambata a baya, sai ka duba wayar domin ka tabbatar ta bushe. Idan kaga alamar bata bushe ba, sai ka ƙara barinta ta bushe.

12. Ka gwada kunna wayar. Ka mayar da batirin sai ka kunna wayar. Bayan ta kama sai ka tabbatar cewa komai yana aiki kama daga speaker zuwa screen da sauransu.

13. A saka a chaji. Idan ka gwada kunna wayar bata kama ba sai a saka ta a chaji. Zai tabbatar maka idan wayar ce ta lalace ko kuma daga batirinka ne. 

14. A kaiwa mai gyara. Idan duk ka gwada abubuwan dana ambata a sama kuma bata kama ba. To sai ka kaiwa mai gyaran waya domin ya duba abinda ya lalace a jiki.
Kar kayi abubuwan nan idan wayarka ta faɗa ruwa
* kar ka kunna ta
* kar ka saka ta a fridge
* kar ka saka ta a oven domin ta bushe
* kar ka kaita gaban wuta
* kar ka bubbuga wayar

A taƙaice idan wayarka ta faɗa cikin ruwa ga abubuwan da zaka yi:
* A cire wayar daga cikin ruwan.
* Kar a danna komai a jiki.
* A cire batiri.
* A cire case/gida.
* A cire duk wani ɓangare mai ciruwa.
* Ka tsane wayar da tawul ko tsumma.
* A guji bushe ruwan cikin wayar.
* Kar a kwance wayar.
* A busar da wayar.
* A jira kwana ɗaya zuwa biyu.
* Ka duba ko wayar ta bushe.
* Ka gwada kunna wayar.
* A saka a chaji.
* A kaiwa mai gyara.


No comments:

Post a Comment