Wednesday, 19 December 2018

Yadda Zaka Ji Sanyi A Motarka Ba Tare Da AC Ba

Shin na'urar sanyi (AC) ta cikin motarka bata yi ne? Ko kuma bata sanyi yadda ya kamata kuma gashi a lokacin zafi ake? Wannan rubutun zai koya maka hanyoyin da zaji sanyi a motarka ba tare da AC ba. Lokacin da ake zafi a waje, cikin motarka yana fin zafi, musamman idan ba ka da AC.
1. Ka saka jiƙaƙƙen tsumma a wurin da na'urar sanyi (AC) mota take. Idan na'urar sanyi (AC) na moatrka bata aiki wato kawai iska take bayarwa, sai ka jiƙa tsumma a ruwan sanyi ka ɗora shi akan bakin na'urar sanyi (AC) ɗin. Yana da kyau idan zaka sami tsummokara da yawa domin ka dinga chanzawa akan kari. Hakan zai dinga baka iska mai daɗi a cikin motar.

2. Ka dinga shan abu mai sanyi. Yana da kyau ka dinga shan ruwa idan ana zafi ba sai kaji ƙishin ruwan ba. Idan baka san ruwa to sai ka samu abu mai sanyi ka dinga sha. Saboda jikinka zai dinga amfani da wannan ruwan domin ya hana ka jin zafin sosai. Idan kana son kayi ajiyar ruwan sanyi sai kayi amfani da flask na shayi don gudun kar ruwan ya huce da wuri musamman idan kana doguwar tafiya.

3. A saka ƙanƙara a ƙasan motar. Yana da kyau ka duba motarka domin gano duk inda ƙofofin na'urar sanyi (AC) na motarka suke. Wasu motocin suna zuwa da ƙofofi har a ƙasan inda zaka saka ƙafarka. Saboda haka, idan kana da kofar AC a ƙasan motarka sai ka saka ƙananun ƙanƙara a ckin mazubin roba kusa da bakin AC ɗin. Idan doguwar tafiya zakayi sai kazo da ƙananun ƙanƙarar da yawa domin chanzawa idan ta narke. Domin gujewar kar ruwa ya ɓata maka mota sai ka saka ƙanƙarar a cikin abinda bazata zube ba.

4. Sanya ruwan sanyi ko kankara akan wuyan hannu da bayan wuyanka. Waɗannan wuraren sune ginshiƙan nunfashi a jikin mutum. Saka abu mai sanyi a kan waɗannan wurare za su kwantar da jin zafi da wuri. Idan ba zaka iya sakawa ba sai kayi amfani da bun fesawa domin ka dinga fesa ruwa mai sanyi a waɗannan wuraren. Idan ma hakan zai maka wahala, zaka iya amafani da tsumma ka saka shi ruwan sanyi domin dora shi a wuraren a dana ambata a baya.
5. Ka saka kaya masu haske. Yau da gobe zaka iya ganowa cewa kaya masu haske basa riƙe zafi kamar waɗanda suke da duhu. Misali anan shine tsakanin baƙar riga da kuma farar riga, kowa yasan cewa baƙa tafi ɗaukar zafi. Idan doguwar tafiya zakayi sai zaka iya ajiye wasu kayan a cikin motar domin ka chanza idan ka fara zufa, hakan zai rage maka jin zafi sosai.

6. Ka sakawa motarka tinti a gilasai. Sakawa mota tinti a jikin gilasai yana rage yawan rana da take shigowa cikin motarka. Amma kafin kayi hakan zaifi kyau idan ka duba dokokin ƙasar da kake ko hakan ya halatta. Wani abin so game da tinti a jikin gilashi shine zai sa kar cikin motarka ya ƙode da wuri.

7. Ka zaɓi kaya marsa nauyi domin ka saka a jikinka. Yau da gobe zaka iya ganowa cewa kaya da suka matse jiki suna riƙe zafi sama da waɗanda basu matse jiki ba saboda babu hanyar da iska zata dinga fita sabuwa tana shigowa. Saboda haka sai a kiyaye irin kayan da zaka saka musamman idan zakayi doguwar tafiya.

8. Zaka iya cire takalman ka idan zakayi tuƙi. Cire takalama a wasu ƙasashen duniya shari'ar ƙasar bata bada adama ba. Kafafuwan mutum suna taka muhimmiyar rawa wajen jin zafi ko sanyi a jiki, saboda haka kar ka rufe su da safa ko kuma takalmi wanda ya matse sosai. Amma idan shari'a bata baka damar tuƙi a haka ba, sai ka saka slipers ko kuma sandal. Amma ka tabbabtar babu abu mai kaifi a ƙasan motar kamar wuka, reza, sukun direba ko gilashi.

9. Yin amfani da fanka ƙarama. Zaka iya siyan ƙaramar fanka ka saka ta akan dashboard ɗinka domin ta dinga baka iska mai sanyi yayin da kake tafiya a moatarka. Idan kana son iskar tayi sanyi sosai sai ka saka jiƙaƙƙen tsumma a saman fankar kamar yadda aka ambata a baya. Yana da kyau idan zaka sami fanka da take da amfani da hasken rana wato ‘sola’ kaga kenan kana tafiya tana chaji.
10. Sauke gilashi domin bawa iska damar shigowa cikin motar. Ya danganta da yadda kake son iska ta shigo cikin motar sai ka sauke gilasan dai-dai da ra’ayinka. Amma ka sani cewa sauke gilashi guda ɗaya kachal yana jawo iska mai zafi a cikin motar. Saboda haka sai ka ɗauki mataki.

11. Ka paka motarka a cikin inuwa ko kuma inda babu rana sosai. Idan zaka ajiye ta ne a wajen biyan kudi sai kayi hasashen inda rana zata koma, sai ka ajiye motarka a wajen. Sannan kuma ka sauke gilasan motar kaɗan domin iska ta dinga shiga cikin motar.

12. Idan zaka iya tafiya da safe ko da dare zaka fi jin daɗin tafiyar taka. Saboda haka ka kiyaye lokutan tafiya idan da dama.

13. Ka guji tafiya a titin da kasan zaka haɗu da go slow sosai. Go slow idan yana tafiya ba matsala bane sosai, amma idan ana daɗewa kafin ya motsa to zaifi kyau ka guje shi. Akwai lokutan da mutane sukafi hada-hada da yawa a cikinsa, misali daga karfe 7-9 na safe, da kuma karfe 4-6 na yamma. A waɗannan lokutan masu makaranta, wajen aiki kasuwa da suransu suke tafiya ko dawowa gida.
A taƙaice:
Domin ka samu sauƙi daga zafi a cikin motarka idan baka da AC sai kayi amfani da waɗannan matakan:
* Ka saka jiƙaƙƙen tsumma a wurin da na'urar sanyi (AC) mota take.
* Ka dinga shan abu mai sanyi.
* A saka ƙanƙara a ƙasan motar.
* Sanya ruwan sanyi ko kankara akan wuyan hannu da bayan wuyanka
* Ka saka kaya masu haske.
* Ka sakawa motarka tinti a gilasai.
* Ka zaɓi kaya marsa nauyi domin ka saka a jikinka.
* Zaka iya cire takalman ka idan zakayi tuƙi.
* Yin amfani da fanka ƙarama.
* Sauke gilashi domin bawa iska damar shigowa cikin motar.
* Ka paka motarka a cikin inuwa ko kuma inda babu rana sosai.
* Tafiya da safiya ko rana idan da halin yin hakan.
* Ka guji tafiya a titin da kasan zaka haɗu da go slow sosai.

No comments:

Post a Comment