Tuesday, 25 December 2018

Yadda zaka gyara naurar sanyin motarka (A/C)

gyaran AC na mota
Mafi yawa daga cikin mutane suna so suji sanyi a motarsu, hakan bazai yiwu ba kuwa sai kana da na'urar sanyin (A/C) a cikin motar kuma tana aiki yadda ya kamata.

1. Ka kunnan motar sannan ka kunna na'urar sanyin (A/C) ka kaita karshe a sanyi. Sai ka ji yadda sanyin yake, shin haka sanyin ya kamata? Ko kuma yayi dumi da yawa? Ko kuwa iska ce kawai take fitowa? Hakan zai baka damar gane matsalar ko daga fitowar iskar ne.
Sai ka duba fankokin jikin radiator suna aiki nko basa yi. Idan basa aiki to lallai matsalar daga wiring ne.
Kila kana buƙatar ka maye gurbin air filter dinka don fitowar sanyin ya haɓaka iska.

2. Duba don ganin cewa kompresor din na'urar sanyin (A/C) yana aiki kuwa. Hakan zai baka damar sanin matakin da zaka dauka idan shine yake jawo matsalar. Zaka gano wurin da na'urar sanyin (A/C) take a cikin injin, idan ka leqa zaka ga wani inji da belt a jikinsa (kamar yadda yake a hoton sama), ka duna ko yana juyawa da injin a jikinsa ko baya yi.

Sannan ka duba kulochi da yake fara aiki idan na'urar sanyin (A/C) tana aiki. To idan kulochin yafara aiki zaka ga tsakiyar wannan injin yana juyawa tare da daya injin a jikinsa.
Idan kulochin bai fara aiki ba, hakan yana nufin kompresor din na'urar sanyin (A/C) bata aiki, kenan tana bukatar chanji ko kuma na'urar sanyin cikinta za’a zuba.3. Bincika wiring din wuta da yake kaiwa kompresor wuta. Yawancin kompresor suna da waya ta wuta da take kaiwa wajen kulochin nan, sai ka nemo hadin da yake tsakiyar wannan wayar ka cire ta. Ka samu doguwar waya ka jona ta daga kompresor din zuwa (+) na batirin motar, idan kaji kara kamar (CLACK) to kulotchinka yana aiki, amma idan ba haka ba yana bukatar a chanja shi. Amma ka sani cewa masu gyaran mota ne kawai zasu iya gyara maka kompresor ko kulochinnan, saboda yana buqatar kayan aiki. Saboda haka, sai ka kaiwa mai gyara.

4. Idan matsalar bata buqatar ganin mai gyaran mota, sai ka duba pipe na na'urar sanyin (A/C) domin ganin ko akwai wajen da yake digowa. Zaka iya siyan wata na’ura da zata taimaka maka wajen gano wannan a wajen masu siyar da kayan mota. Ita wannan na’urar zata shiga cikin pipe dinne ta nuna maka wajen da ya toshe ko kuma yake diga. Idan kaga cewa yana diga to lallai sai ka kaiwa masu gyara idan kuma baka ga komai ba to matsalar da karancin abunda yake sata sanyi ne wato refrigerant.

5. Sai ka siyo refrigerant da yake dai-dai da motarka domin ka qara a cikin motar. Hanya mafi sauqi da zaka gano wana irin refrigerant zaka siya shine ka duba shekarar da akayi motarika. Dukkan motar da aka gina bayan 1995 suna yin amfani ne da R134a. Idan motarka tafi haka tsufa to sai kayi amfani da R12.
Matsalar anan itace, baza ku iya cika R12 refrigerant da kanka ba.

6. Ka nemo ajen da ake kira da low-side service port a jikin na'urar sanyin (A/C) din. Ka duba hoto na sama domin karin bayani. Zaka gansu guda biyu ne, daya a sama dayan kuma a kasa. 

To na kasan shin ake kira da low-side service port din. Domin nemo shi sai kabi pipes/layukan da suka fito daga kompresor din na'urar sanyin (A/C) har sai kaga wani kofa da mai murfi a kusa da kasan motar. Idan ka kasa nemowa sai ka karanta littafin daya zo da motarka.
7. Yi amfani da tsumma mai kyau domin goge bakin service port din. Ka tabbatar cewa baka toshe kofar ba ba tarkace ko datti a kofar ba.

8. A wannan matakin sai ka jona bakin mesar da tazo da refrigerant a bakin low side port din, ka tabbatar cewa daya bakin mesar tana hade da gwangwanin refrigerant din. Yana da kyau idan mesar doguwa ce domin kar ka dinga saka gwangwanin refrigerant din a cikin injin motar.

9. Kayi amfani da makunnin dake jikin gwangwanin refrigerant din domin kunna shi har sai kaji abinda ya toshe gwangwanin ya bude. Yawancin gwangwanayen dama ake juya su domin a bude kan nasu, amma zaka iya duba takardar da tazo dashi domin yadda ake.

10. Riƙe gwangwanin a tsaye domin refrigerant din ya shiga cikin A/C din yadda ya kamata, sannan ka dinga girgiza shi lokaci bayan lokaci domin abubuwan cikinsa su hadu da kyau.
Kar ka kuskura ka juya gwangwanin sama ya koma kasa yayin amfani dashi.

11. Ka duba kaga ko akwai wajen da yake diga. Idan kaga wajen da yakke diga to gyaransa sai an kai wajen mai gyara. Sai ka gane wajen da yake digar domin saukin gyarawa.
12. Cire mesar da take bada refrigerant din idan injin ya cika, sannan ka mayar da murfin ka rufe lower service port din. Sannan ka boye gwangwanin a wajen mara zafi saosai. Amma idan babu komai a cikinsa sai ka yar da shi.

No comments:

Post a Comment