Tuesday, 25 December 2018

Yadda Ake Katange Lambar Sadarwa A Kan Whatsapp

katange block lambar whatsapp

A wannan lokacin zamu koyi yadda ake blockin lambar sadarwa daga yi maka saƙo akan hanyar sadarwa ta WhatsApp, zaka iya mafani da wannan hanya akan android, iphone da kuma komputa.
Hanyar ta Ɗaya
A kan wayar iPhone

1. Buɗe WhatsApp. A cikin wayarka ta iphone sai ka danna WhatsApp domin ya buɗe. Domin ka gane shi, zaka ganshi yayi kama da alamar kira fari a cikin koren alamar magana. Hakan zai buɗe maka ƙarsheninda ka tsaya a cikin sa.

2. Matsa Saituna (settings). Yana nan a ƙasa cikin kusurwar dama.
Amma idan WhatsApp ɗin ya buɗe maka tattaunawar hira ne da farko, sai ka danna maɓallin "Back" a saman kusurwar hagu na na wayarka.

3. Sai ka danna inda kaga an rubuta ‘Account’. Wannan yana kusa da saman shafin Saituna.

4. Sai ka danna ‘Privacy’. Yana nan saman shafin ‘Account’ daka shiga.

5. Sai ka danna ‘blocked’ wato katange. Za ku ga wannan a kusa da kasan shafin ‘Privacy’ daka shiga. Yin hakan zai buɗe jerin lambobin sadarwar da ka katane (blocking)

6. Sai ka danna ‘Add New…’ wato Ƙara Sabo. Yana nan a saman shafin. Amma Idan kana da wasu lambobin da aka katange, zaka ga ‘Add New…’ din a kasa sunayen da aka katange.

7. Sai ka zaɓi lambar da zaka toshe/katange. Ka danna sunan wanda kake son toshewa don ƙara su zuwa jerin labobin daka katange a da.

8. Buɗe katangewar idan kaga cancantar hakan. Idan kana so ka cire katangar, yi waɗannan a bubuwan:
- Matsa ‘Edit’ a saman kusurwar dama na shafin "Blocked".
Matsa jan da'irar hoto da zaka gani a gefen hagu na sunan lambar da kake son cirewa.
- Matsa ‘Unblock’ dake dama da sunan mutumin.

9. A katange/toshe lambar sadarwa daga hira (chatting). Idan kana so ka toshe wani wanda baya a cikin lambobinka, za ka iya toshe su daga cikin saitunan hira (chatting):
- Matsa hirar da kake da mutumin da kake son toshewa.
- Matsa suna ko lambar a saman shafin hirar.
- Sauko ƙasa ka danna ‘Block Contact’.
- Ka danna Block lokacin da aka nuna maka hakan.
Hanyar ta biyu
A kan wayar Android

1. Buɗe WhatsApp. Ka dannan icon na WhatsApp dake jikin screen ɗinka. Zaka ganshi da farin alamar kira, a cikin koren alamar magana. Hakan zai buɗe WhatsApp ɗin a inda ka tsaya a ada ko kuma ya buɗe maka hirarrakin da kayi.

2. Matsa digo guda uku. Zaka ganshi a cikin kusurwar dama na shafin farkon. Amma idan WhatsApp ɗin ya buɗe shafin taɗinka na ƙarshe, to sai ka danna "Back" kafin ka latsa ɗidon nan guda uku.

3. Danna Saituna (settings). Wannan shine a ƙarshen ƙaramin shafin da zai buƙe.

4. Sai ka danna ‘Account’. Yana nan a farkon shafin (settings)

5. Ka danna ‘Privacy’. Za ku sami wannan a saman shafin ‘Account’.

6. Matsa ‘Blocked contacts’. Yana kusa da asalin shafin Sirri wato ‘Privacy’. Yin hakan zai buɗe maka jerin mutanen daka toshe/katange.

7. Matsa "Add". zaka ga wannan a matsayin hoton mutum da alamar + a gabansa, yana nan a cikin kusurwar dama na allon. Yin hakan zai buɗe adireshin lambobinku na Android.

8. Zaɓar lamba. Matsa lambar sadarwa wanda kake son toshewa/katangewa. Yin hakan nan da nan zai saka mutumin zuwa jerin mutanen daka katange

9. Buɗe katangewar da kayi idan kana so. Idan kana so ka cire katangar, yi wadannan:
- Yi dogon dannawa akan sunan/lambar a kan shafin "Lambobin da aka katange".
- Matsa ‘unblock name’ idan hakan ya fito.

10. Katange lamba daga hira. Idan kana so ka toshe wani wanda ba a cikin lambobinka ba, za ka iya toshe su daga cikin saitunan hirarku:
- Shiga hirar da kukayi tare da mutumin da kake son toshewa.
- Matsa sunansa/lambar dake saman shafin.
- Gungura ƙasa sannan ka danna Block a ƙasan shafin.
- Matsa 'BLOCK' lokacin daya fito.No comments:

Post a Comment