Tuesday, 25 December 2018

Yadda Ake Farfesun Kaza

farfesun kaza
Abubuwan da ake buƙata:
Kaza
Attarugu (4)
Albasa (2)
Maggi (4)
Cittah
Tafarnuwa
Kori
Gishiri

Abubuwan daya kamata ki sani kafin kiyi farfesun kaza:
- idan zakiyi wannan girkin, zaifi kyau idan zakiyi amfani da kaza gaba ɗayanta. Ki yayyanka dukkan ɓangarorin sannan ki wanke ta.
- idan zaki yanka albasa, zaifi idan kika yanka ta ƙanana.
Yadda ake haɗawa:
- Da farko Uwargida idan aka yanka miki kazarki ki gyarata da kyau kisa a tukunyarki sannan ki zuba ruwa ya rufe ta.
- Bayan nan sai ki yanka albasa ƙanana sannan ki sa maggi da cittah ki rufe yayi 'yan mintuna.
- Idan ruwan ya ragu, wato ta fara dahuwa, sai ki daka attarugu da albasa ki zuba ki sa cittah, tafarnuwa, maggi, gishiri da kori, sai ki juya har sai komai yayi sai ki rufe ki barshi ya dahu.
- Idan yayi sai ki sauke.
- Yawancin mutane sunfi son suci farfesun da zafinsa. Sannan kuma za'a iya cinsa da shinkafa ko kuma shi kaɗan da lemo mai sanyi.

No comments:

Post a Comment