Saturday, 29 December 2018

Yadda Ake Duba Sakamaon Jarrabawar WAEC

jarrabawar waec

Domin duba sakamakon jarrabawar WAEC sai a biyomu sannu a hankali.

Akwai hanyoyi biyu da ake iya duba sakamakon jarrarbawar:
- Hanya ta farko itace amfani da SMS
- Hanya ta biyu itace amfani da shafin yanar gizo.

Abubuwan da ake bukata:
- Lambar jarrabawa (Examination Number). wannan itace lambar da kowanne dalibi yake da ita kuma lambobi goma ne. Misali 1234567897
- shakar da aka rubuta jarrabawar (Examination year). Ya danganta da shekarar daka rubuta jarrabawar. Saka shekarar zaisa ka samu sakamakonka da sauki daga shafin yanar gizon.
- Kalar jarrabawar (Examination type). akwai jarrabawa kala-kala kamar SSCE, GCE da sauransu. Saboda haka idan jarrabawar WAEC zaka duba to sai ka zabi SSCE.
- Katin duba jarrabawa.
- Serial Number jikin katin.
Domin duba jarrabawar WAEC ta sakon waya (SMS)
1. A tura sako a jadawalin dake kasa
WAEC*LambarDalibi*PIN*ShekararJarrabawar
2. Sai a turawa 32327
3. Sai a jira sakamakon jarrabawar a cikin wayar.
4. Amma zasu ciri N30 kudin dubawa.

Domin duba sakamakon ta yanar gizo:
1. A shiga shafin yanar gizo na http://waecdirect.org
2. Sai a saka lambobi guda goma na dalibin. (lambobi bakwai din farko na wajen dakayi jarrabawar ne, lambobi ukun karshe kuma na dalibin ne).
3. Sai a rubuta shekarar da akayi jarrabawar, misali 2007.
4. Sai ka zabi kalar jarrabawar .
5. Sai kuma a saka seriel number dake jikin katin da aka kankare na duba jarrabawa.
6. Sai a saka PIN wanda ke jikin katin duba jarrabawar.
7. Sai a danna Submit a jira sakamakon ya bude.No comments:

Post a Comment