Saturday, 29 December 2018

Yadda Ake Daina Minshari Idan Ana Bacci

daina minshari a bacci

Yin minshari idan mutum yana bacci bashi da dai ko kadan musamman idan ba kai kadai kake kwana a cikin dakin ba. Amma kuma mu gane cewa mutane da yawa sunayin mishari idan suna bacci, idan ya zamana kullum kana cikin mishari ne kuma kusan ko wanne lokaci, to hakan ya zama matsala kuma. Akwai matsala idan har misharinka yana iya tashin wani daga bacci. 

1. Ka chanja yadda kake kwanciya. Idan kana kwance ne a gadon bayan ka to lallai kuwa zakayi iya yin munshari kamar yadda binciken masana ya nuna. Saboda haka sai a gyara idan ka san kana bacci a wannan yanayin. Kuma idan mutum ya fahimci kwanciyar bacci a musuluci zai san cewa ba haka akeyin bacci ba.
Sannan idan bakasan ka dinga kwanciya akan gadon bayan ka, zaka iya dauri abu kamar kwallon goruba a bayan naka, ta yadda duk yayin da ka juya zakaji baccin babu daɗi saboda haka dole ka juya zuwa gefe.

2. Ka rage kiba. Rage kiba yana taimakon mutane da yawa wajen daina munshari, amma kuma wasu baya yi musu saiki. Ka lura idan ka kasance baka minshari kafin kayi kiba ko kuma sai bayan kayi kiba ne ka fara misharin? Idan sai bayan kayi kiba ne ka fara, to rage kibar zai iya taimaka maka wajen daina mishari. Ita kiba masana lafiyar dan Adam sun nuna cewa bata da wani amfani ma a jikin mutum sai dai ma cututtuka da take kawo masa kala-kala
3. Daina shan giya. Ina tinanin wannan ba sai munyi dogon bayani a kansa ba. Kowa ya sani cewa shan giya ba abune mai kyau ba. Kuma idan muka dauki musulunci da kiristanci ai duk sun hana mu shan giya. Idan mutum yana shan giya kamar awa hudu kafin ya kwanta, to lallai mishari zaiyi mara dadi kuwa.

4. A daina shan sigari (taba). idan mutum ya kasance yana shan taba, to tallai yana da haɗarin kamuwa da minshari idan yana bacci. Hakan yana faruwa ne saboda hayaƙin taba yana lalata hanyoyin da iska take bi a jikin mutum har wani lokaci su toshe. Idan kana samun wahalar daina shan taba, kayi magana da likitan ka domin ya taimaka maka da abubuwan da zasu saka daina sha.

5. A chanja pilon kwanciya. Idan kasan pilon da kake kwanciya baka wanke shi yadda ya kamata. Ko kuma ma baka taba wankeshi ba, to lallai zai iya jawo maka mishari idan kana bacci saboda kwayoyin dake taruwa a jikinsa. Abu na gaba shine ka rage dabbobin dake shigowa dakin kamar mage. Suma zasu iya jawo abinda ake kira da allergy wanda zai iya saka maka minshari musamman idan suna hawa pilon da kake kwanciya. Bayan nan akai wani pilo da ake siyar domin mutanen dake fama da minshari idan suna bacci. Matsalar wannan pilon shine ba kowa yake yiwa aiki ba.

6. Ayi magana da likita. Mishari a bacci idan yayi yawa to ana zaton cewa wata cuta ce take kawo shi. Saboda haka yana da kyau idan kaje ganin likita domin magance wannan matsalar. Sannnan kuma kayi kokarin fadamasa duk wata matsala dake damunka kamar hawan jini, rashin bacci, ciwon kirgi da sauransu.
A takaice a lura da wandannan abubuwan:
- Ka chanja yadda kake kwanciya.
- Ka rage kiba.
- Daina shan giya.
- A daina shan sigari (taba).
- A chanja pilon kwanciya.
- Ayi magana da likita.

No comments:

Post a Comment